Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Zan Iya Sa Ma Mijina Guba’ Inji Wata Mata A Gaban Kotu

Published

on

Wata matar aure mai suna Ronke Olanrewaju mai ‘ya’ya uku da ke zaune a garin Ibadan ta neme wata kotu da ta kawo karshen auren ta da mijinta, a yau Laraba.

Dadin dadawa matar ta yi barazanar amfani da guda don hallaka mijin nata mai suna Sunday, muddin dai kotun ba ta kawo karshen zaman nasu ba, saboda a cewarta ta gaji da ci mata mutumci da Sunday yake yi a kullum.

A takardar karar da ta shigar gaban kotu, Ronke mai sana’ar saye da siyarwa ta ce ita ta gaji da yadda mijinta yake lakada ma ta dukan tsiya a kullum, wanda hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta kwaci kanta daga hannun shi.

‘Gaba daya ya sa min da na sanin auren shi da na yi, duk lokacin da wani namiji ya shigo shago na don siyan wani abu, sai Sunday ya hasala ya zarge ni da aikata masha’a da masu ciniki na.’ inji Ronke

Ronke ta kara da: Kullum sai ya lakada min doka ba gaira ba dalili, haka zai ta bugu na ba ko tausayi, kuma abun haushin ma shine, abun nashi bai tsaya a bugu na kadai ba, har mahaifiyata yana lakada wa duka kamar ‘yar shi, yak an kulle ni a daki, saboda a cewar shi shi dan siyasa ne don haka yafi karfin doka.

‘In dai wannan kotun ba ta kawo karshen auren nan ba, toh tabbas zan sanya mishi guba a abinci don in hallaka shi.’ Inji Ronke

Sunday da ake kara dai ya karyata duk zarge-zargen da matar shi ronke ta ke mishi, inda yace kotu ta roke ta ta yi hakuri, zai ma sanya hannu a yarjejeniyyar cewa ba zai sake taba ta ba.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: