Zan Iya Tattaunawa Da Real Madrid, Cewar Hazard

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard ya bayyana cewa a shirye yake daya tattauna da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid idan har sunje sun fara tuntubar kungiyarsa ta Chelsea akan ko zai koma kungiyar.
Sai dai dan wasan kawo yanzu bazai yanke hukuncin zama ko barin kungiyar ba har sai yaga yadda kungiyar za ta karke da mai koyar da kungiyar Antonio Conte saboda yanason sanin halin da kungiyar za ta shiga.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta dade tana zawarcin dan wasa Hazard musamman lokacin tsohon kociyan kungiyar Zidane wanda yace dan wasan yana burgeshi kuma yanason suyi aiki tare a kungiya daya.
“Inson sanin makomar mai koyarwar kungiyar idan zai zauna to idan kuma wani za a kawo to sannan kuma inason sanin inda kungiyar za ta fuskanta idan akwai alamar gyara zan zauna idan kuma naga akwai matsala zan sake tunanin” in ji Hazard
Yaci gaba da cewa Real Madrid za ta iya nemansa kuma kowa yasan haka kuma za ta iya cewa batasonsa amma kuma ya danganta da yadda abubuwa suka tafi bayan kammala gasar cin kofin duniya
Hazard dai yana kasar Rasha inda yake wakiltar kasarsa ta Belgium a gasar cin kofin duniya kuma tuni suka buga wasa da kasar Panama inda suka samu nasara daci 3-0 a wasan farko da suka fafata kuma zasu buga da kasar Ingila da Tunusia a wasanninsu na gaba.

Exit mobile version