Daga Mustapha Ibrahim,
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya da ke Abuja Nijeriya, kuma mataimakin shugaban yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya garambawul, Hon. Alhassan Ado Dogowa, ya bayyana cewa, zai kai kudirin yin dokar da za ta hana ‘yan kwaya masu ta’ammali da sha da fataucin miyagun kwayoyi hana su rike ko wane irin mukami a Tarayy ar Nijeriya.
Hon Alhassan Ado Dogowa ya bayana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Rano a karshen makon da ya gabata ya ce a matsayinsa na dan majalisa a yanzu zai amfani da wannan dama ta sa wajen ganin an sa wannan kudiri nasa na ganin cewa an haramta wa dukkan wani dan kwaya rike kowane irin mukami na siyasa, domin wannan shi ne zai tamakawa hukumar NDLAE aikin da ya gagari kwandila ko kuma ya gagari dukan wani mai kokarin hanawa kamar ‘yan sanda, alkalai, Malamai masu wa’azi da dai sauransu. Kuma yin hakan duk zai magance wannan matsala musamam ga dukka wani matashi ko dan Nijeriya da ke san rike wani mukami don taimakawa kasarsa da sauran al
ummar Nijeriya,
Sannan ya ce yana da kyakyawan zato cewa wannan kudiri na doka zai samu kyakyawan goyan baya daga ‘yan uwansa ‘yan majalisa. domin gyara al`umma aikin duk shugaba ne na gari da yin umarni da kyakkyawa.
Hon Alhassan Ado Dogowa wanda shi ne ya jagoranci kula da harkar zaben kananan hukumomi Kano a masarautar Rano ba bayyana gamsuwarsa kan yadda zaben kananan hukumomin ya gudana lami lafiya a Jihar Kano baki daya.