Zan Karya Tarihin Rashidi Yakini A Nijeriya -Osimhen

Yakini

Victor James Osimhen of Nigeria during the 2019 Africa Cup of Nations Finals, 3rd and 4th place match between Tunisia and Nigeria at Al Salam Stadium, Cairo, Egypt on 17 July 2019 ©Samuel Shivambu/BackpagePix

Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasan gaba ba kungiyar kwallon kafa ta Napoli, kuma dan Najeriya Victor Osimhen ya bayyana aniyarsa na zarce irin banjintar da tsohon gwarzon dan wasan kasar nan Rashidi Yekini ya yi a wajen cin kwallaye a babbar tawagar kwallon kafar kasarsa ta Super Eagles duk da cewar ‘kamar da wuya’.

Har yanzu dai babu dan wasan Najeriya da ya kai Rashidi Yekini saka kwallo a raga, inda ya zura kwallaye 37 daga wasanni 58 daya bugawa Super Eagles, kuma ya taimaka wa tawagar ta taka rawar gani a gasannin kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu, Osimhen ya zura kwallaye hudu ne a raga daga cikin wasanni 10 da ya buga wa Najeriya tun da ya fara wa tawagar Super Eagles wasa a shekarar 2017 kuma yayi alkawarin karya tarihin na Yakini

“Rashidi Yakini dan wasa ne wanda a tarihin kwallon kafar kasar nan ba za’a taba mantawa dashi ba idan aka duba irin nasarorin daya samu da kuma irin nasarar daya taimaka tawagar ta samu a lokacinsa” in ji Osimhen

Ya ci gaba da cewa “Komai zai iya faruwa a yanzu saboda ina da lokacin da zan iya kamo yawan kwallayen daya zura a raga da kuma irin bajintar da tawagar ta nuna gaba daya a lokacin da suka rubuta sunan kasar nan a idon duniya a fannin kwallon kafa”

Dan wasan mai shekaru 21 a duniya ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki tukuru don ganin ya zama dan wasan da ya fi ci wa tawagar Super Eagles ta Najeriya kwallo a tarihi, sai dai ya ce lallai ba abu ne mai sauki ba.

Osimhen ya taka mahimmiyar rawa a karawar da ta gudana tsakanin Najeriya da kasar Sierra Leone a Juma’ar nan a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika wasan da aka tashi 4-4.

Exit mobile version