Zan Kawo Gyara A Juventus, In Ji Allegri

Allegri

Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Massimiliano Allegri, ya bayyana cewa zai kawo wasu canje-canje a kungiyar wanda zai kawo gagarumin ci gaban da zaai saka kungiyar akan turba.

A ranar Lahadi ne kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sake daukar tsohon kocinta Massimiliano Allegri awanni bayan ta kori Andrea Pirlo daga koyar da ‘yan wasan kungiyar ta birnin Turin.

An yi mamakin yadda aka zabi tsohon dan Italiya mai shekara 42 lokacin da ya maye gurbin Maurizio Sarri a kakar wasa ta bara saboda rashin kwarewarsa wajen koyar da manyan kungiyoyi a duniya.

Juventus ta kare kakar wasa ta Serie A na bana a matsayi na hudu karkashin tsohon dan wasanta, wannan ne karon farkon da kungiyar ta kasa cin wani kofi tun shekarar 2012 kuma a karkashin Andrei Pirlo.

Allegri shi ke rike da kungiyar Juventus tun daga shekarar 2014 zuwa 2019, ya lashe kofin Serie guda biyar a jere, ya kuma ci Coppa Italia tare da zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun turai Champions guda biyu.

“Bisa ga jajircewa da kwarin gwiwa da ya nuna a kowacce rana, muna jinjina ga ‘Gwarzo’,” a cewar wata sanarwa da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta wallafa a shafinta na intanet bayan sanar da korar.

Kungiyar ta kare kakar bana a matsayi na hudu a teburin Serie A kuma har sai a wasan karshe sannan ta samu damar shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League inda tuni Massimiliano Allegri ne zai maye gurbinsa a matsayin koci karo na biyu sai dai kakar wasa  daya kacal Andrea Pirlo yayi yana jagoranci Juventus

Allegri ya jagoranci kungiyar daga 2014 zuwa 2019, inda ya lashe kofin Serie A sau biyar a jere sannan ya kai ta wasan karshe a Champions League sau biyu sai dai tun bayan barin sa Juventus bai koyar da kowacce kungiya ba duk da cewa kungiyoyi irinsu Real Madrid sun nemeshi.

Andrei Pirlo ya buga wa Juventus kwallo daga shekarar 2011 zuwa 2015, inda ya lashe Serie A hudu bayan ya koma daga AC Milan sannan ya taimaka wa kasarsa Italiya lashe Kofin Duniya na shekarar 2006 kafin ya yi ritaya a shekarar 2017 bayan ya buga mata wasanni  116.

Exit mobile version