Khalid Idris Doya" />

Zan Kawo Karshen Talauci A Nijeriya, Inji Farfesa Moghalu

Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Dan takarar kujerar shugaban kasa, Farfesa Kingsley Moghalu, ya bayyana cewa, idan har Allah ya yarda ya samu nasara a zabe mai zuwa, gwamnatinsa za ta yi kokarin shawo kan matsalar talauci da ya yi wa Nijeriya katutu.

Farfesa Moghalu ya bayyana hakan ne jiya a garin Makurdi a lokacin da ke ganawa da al’ummar Jihar Binuwai.

Farfesan ya ce, daga cikin abubuwan da zai sanya a gaba gami da neman kawo karshensu akwai tabbatar da inganta sha’anin tattalin arzikin Nijeriya, hade da tabbatar da samar wa kowanne dan Nijeriya jari da kuma yadda zai yi domin bunkasa tattalin arzikin kashin kansa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Babban Bankin Nijeriyan ya kara da cewa, dalilansa na fitowa neman shugabancin Nijeriya ba komi bane face don samar da ci gaba ga kasar. “Domin mu samu gina kasa da kuma kyautata kasar,”

Ya kuma sha alwashin cewa, zai kawo wa kasar nan ci gaba sosai musamman ta hanyar siyasa da kuma kokarin shawo kan rikicin manoma da makiyaya da ke ci gaba da addabar Nijeriya. Ya ce, yin hakan zai kawo karshen matsalolin da suke dakile kokarin da ake yi na gina kasa.

A cewar sa; “Za mu yi kokarin kawo karshen yawan kashe-kashen da ake samu a Nijeriya, sannan kuma zan tabbatar da kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da sauran matsalolin tsaro da suka addabi Kasar nan.”

 

 

Exit mobile version