El-Mansur Abubakar" />

Zan Kawo Kyakkyawan Tsari Idan Na Zama Shugaban Maganin Gargajiya Na Gombe – Sa’idu Wanzam  

Sarkin Askar Bogo kuma Sintalin Sarkin Askar Gombe, Dakta Sa’idu Wanzam mai Kaciya a sa wando, ya dauki alkawarin kawo kyakkyawan tsari da shirya ajandoji bakwai dan gyara tsarin kungiyar masu maganin gargajiya na jihar, idan ya zama sabon zababben shugaban kungiyar.

Dakta Sa’idu Wanzam, yace akan Ajanda bakwai kawai zai tsaya kuma sai kungiyar ta gyaru muddin ya samu dama aka zabe shi dan ganin ya dawo wa da ‘ya’yan kungiyar mutuncin da aka zubar musu a idon duniya.

Yace Ajanda ta farko ita ce daidai ta tsarin masu magani wajen samar da maganin da kuma yadda za’ayi amfani dashi.

Ajanda ta biyu dawo da martabar masu maganin  gargajiya da kimar da suka rasa a wajen al’umma, ta uku yace za’a dinga shirya bita kan magunguna duk bayan wata uku, ajanda ta hudu zai yi kokari ya daidai ta kungiyar su da hukumar NAFDAC da Ma’aikatar lafiya, ta biyar duk wani shugaba na kungiya za’a ba shi damar ya tafiyar da ofishin sa yadda ya kamata, ajanda ta shida kuma ita ce yadda zai hada kai da wasu mutane dan samarwa da kungiyar ofis na ta na kanta da kuma Motar kungiyar sannan abu na bakwa shi ne yadda za’a zabi shugabni na kowanne yanki na mazabu dari da goma sha hudu na Gombe dan samun sauki wajen sanin adadin masu maganin gargajiya sahihai a fadin jihar.

Sarkin Aska  Sa’idu Wanzam, ya kuma ce saboda daraja kai duk wani bakon dan magani da ba dan jihar ba idan ya shigo sai an san daga inda yazo kuma shi waye ne dan kar ya sayarwa da mutane gaibu ya tafi a dinga jam’I ina zagin masu maganin gargajiya.

A wannan takara tasa yace kullum kara samun hadin kai da goyon bayan masu maganin yake yi domin yanzu haka ma ya yi zama da yan magani na kasuwar Gombe ya bayyana musu manufofin sa sun aminta da su.

Ya kuma ce idan aka dai dai ta komai kungiyar ta zama tana kan tsari za su sa a dinga tsabatce itace tun daga wajen ciro shi a daji har zuwa sarrafa shi da kuma yadda za’a sha a matsayin magani.

A cewar sa wani lokacin za ka ga an zuba magani a kasa waje marar tsabta kuma wata kila tun a daji wani tsuntsu ko kwaro ya yi kashi ko ya zuba yawu a jikin itacen ba’a tsabtace shi ba an zo ana sayarwa jama’a a haka sai wata cuta ta shiga yace za su sa dole a gyara.

Sannan yace bayan an samu tsari har ila yau dattawan kungiya dole su zama suna fada aji a kungiya duk wanda ya saba musu ko ya karya doka kungiya za ta taka shi.

Daga nan sai ya yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da cewa idan suka yi biyayya kungiyar ta kai inda ake so za’a dinga shirya bita na koyar da su hanyoyin sarrafa itatuwa na zamani.

Exit mobile version