Nasir S Gwangwazo">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Zan Raba Tallafi Ga Matan Karkara A Ko’ina – Minista Sadiya

by Nasir S Gwangwazo
December 4, 2020
in LABARAI
2 min read
Zan Raba Tallafi Ga Matan Karkara A Ko’ina – Minista Sadiya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Cewar Minista Sadiya a taron Imo: Za mu raba kuɗin tallafi ga matan karkara ko’ina a Nijeriya

 

samndaads

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi alƙawarin cewa dukkan jihohi 36 da ƙasar nan da kuma yankin Abuja za su amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na Agajin Kyautar Kuɗi ga Matan Karkara, wato ‘Special Cash Grant for Rural Women’.

Ta bada wannan tabbacin ne a wajen taron ƙaddamar da shirin a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ranar Alhamis, 3 ga Disamba, 2020.

Sadiya ta ce, “Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi maida hankali ga matsalolin marasa galihu a ƙasar nan tun daga 2015 kima mutum 150,000 ake sa ran za su ci moriyar shirin ta na bai wa matan karkara tallafin kuɗi a dukkan ƙananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan.

“Tun daga farkon shirin nan na ‘National Social Investment Programme’ a matsayin wani tsari na yaƙar talauci a tsakanin yawanci al’ummar mu, rayuwar talakawa faƙirai a Nijeriya ta inganta sosai. Da yawa daga cikin irin waɗannan mutanen sun samu cikakken sauyin rayuwar su. Saboda haka, ina farin cikin ganin taruwar ku a nan domin ƙaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya na raba wa matan karkara agajin kuɗi, wanda ya na daga cikin shirye-shirye masu yawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu ta fito da su saboda ta ɗaga rayuwar yawancin jama’a daga ƙuncin rayuwa.

Ministar ta ƙara da cewa manufar wannan agajin musamman ɗin ita ce a kai tsabar kuɗi kai-tsaye ga gidajen da su ke buƙata wanda hakan zai taimaka wa iyalan wajen sayen kayan masarufi, yin amfani da kayan magance matsalar yunwa sayen kayan abinci da kula da lagiyar jiki, da shigar da yara da biya masu kuɗin makaranta da dai sauran su.

Ta yi kira a gare su da su yi amfani da kuɗin wajen yin ƙananan kasuwanci wanda hakan zai taimaka wa dogaro da kai da samun sana’a.

Tun da farko, sai da mai ba Gwamnan Imo Shawara kan shirye-shiryen cigaban al’umma na SDGs da ayyukan jinƙai, Gimbiya Christina Udeh, ta ce ziyarar da ministar ta kai a jihar, shaida ce da ke nuna yadda ta ke damuwa da matsalolin tattalin arzikin al’ummar Jihar Imo, ciki har da naƙasassu da faƙirai da ke zaune a yankunan karkara.

Ta ce, “Shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin kuɗi ga matan karkara zai rage fatara da yunwa, ya hana marasa galihu cigaba da faɗuwa cikin ramin fatara da yunwa kuma ya ba su kariya daga bala’o’i.

“Haka kuma ministar ta zo nan ne domin ta ƙaddamar da Ranar Mutane Masu Fama da Nakasa ta Duniya sannan ta raba N20,000 ga kowace macen karkara domin ta ja jari wanda zai taimaka ya sauya mata rayuwar ta da halayya.”

Matan sun bayyana godiyar su ga Shugaba Buhari saboda wannan tsari da ya fito da shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

NIS Ta Karbi Karin Na’urorin Kula Da Shige Da Fice 63 Daga Kanada

Next Post

Kungiyar ‘Tinubu Vanguard’ Ta Ce Sake Naɗin Yakubu A INEC Ya Dace

RelatedPosts

A duniyar Nijeriya ta yanzu, da yawan mutane da ma masu lura da al’amuran yau da kullum su na kallon gudanar da zabukan kananan hukumomi

Abubuwan Al’ajabi A Zaben Kananan Hukumomin Kano

by Nasir S Gwangwazo
4 hours ago
0

Kuri’un Da Aka Kidaya Sun Haura Na Zaben Gwamna A...

Ranar Bude Makarantu

Korona: Har Yanzu Babu Ranar Bude Makarantu A Jihar Kaduna

by Nasir S Gwangwazo
4 hours ago
0

 Dukkanin makarantun Firamare da na sakandari da suke jihar Kaduna...

Kwalejin Kimiyya

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Kwalejin Kimiyya Ta Farko A Borno

by Nasir S Gwangwazo
5 hours ago
0

Ranar Litinin Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai...

Next Post
Kungiyar ‘Tinubu Vanguard’ Ta Ce Sake Naɗin Yakubu A INEC Ya Dace

Kungiyar 'Tinubu Vanguard' Ta Ce Sake Naɗin Yakubu A INEC Ya Dace

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version