Abba Ibrahim Wada" />

Zan Rama Abinda Ruiz Ya Yi Min, Cewar Anthony Joshua

Shahararren dan wasan damben nan na duniya Anthony Joshua ya bayyana cewa yaji bakin cikin rashin nasarar da yayi a hannun Andy Ruiz Jr kuma ya bayyana cewa zai sake farfadowa a wasan da zasu fafata a nan gaba a birnin London.

Joshua, wanda shine zakaran damben Boksin na duniya ya sha kashi a hannun Andy Ruiz, a wata fafatawa da ‘yan wasan biyu suka fafata a babban dakin wasa na Madison Skuare Garden dake birnin New York dake kasar Amurka.

Ruiz ya samu nasarar ne bayan ya samu nasarar doke Joshua a turmi uku a jere bayan da tun farko Anthony Joshua ne yafara samun nasara a turmi na farko wanda hakan ya harzuka Ruiz, wanda yayiwa Joshua fatafata.

“Tabbas banji dadin abinda yafaru ba akaina saboda banyi zaton hakan zata kasance ba saboda a tunanina na gama shiryawa wannan wasa kuma tabbas nayi kokarin ganin nasamu nasara sai dai a wannan lokacin bani da nasara” in ji Anthony Joshua, dan asalin Najeriya.

Ya cigaba da cewa “Andy Ruiz yanzu shine zakara na duniya amma na dan lokaci domin zanyi kokarin ganin na rama abinda yayi min idan muka sake haduwa a wasan da zamu  sake fafatawa a babban birnin Ingila, Landan a nan gaba kadan.

Andy Ruiz dai shine dan kasar Medico na farko daya taba lashe kyautar gwarzon duniya kuma tuni Anthony Joshua ya taya shi murna inda ya bayyana cewa tabbas ya cancanta daya samu nasara saboda yadda ya tunkari fafatawar ba da wasa ba.

Exit mobile version