Daga Khalid Idris Doya, Bauc
Yusuf Mai-Tama Tugga shi ne sabon Jakadar Nijeriya a kasar Jamus wanda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tura a kwakin baya, ya shaida cewar kasar Jamus kasa ce da take fama da yawaitar ‘yan Nijeriya masu yin kaura a sakamakon rashin sana’o’in dogaro da kai, ya ce Jamus ta iya fahimtar hauhawar ‘yan Nijeriya masu yin tururuwa zuwa kasar ta su baya rasa nasaba da rashin aikin yi da Nijeriya ke fama da ita. Ya ce kasar ta himmatu waje samar wa Nijeriya cibiyoyin koyon sana’o’in dogaro da kai. A bisa haka ne ya shaida cewar, zai yi kokari wajen kawo wa Nijeriya ci gaba sosai daga kasar ta Jamani. Ya bayyana hakan ne a wajen taron liyafar taya shi murnar samun mukamin da magoya bayansa suka shirya masa a kwanaki kafin tafiyarsa kama aiki a can Jamus
Da yake amsa tambayoyin manema labaru a wajen taron, Amasada Yusuf Tugga ya ce, matsalar yawaitar ‘yan Nijeriya masu kaura zuwa Jamus zai ragu da zarar a ka samu hanyoyin koyar da sana’o’in dogaro da kai “Idan mutanen mu suka samu abun yi ne kawai za magance wannan matsalar, shi ya sa na ke cewa su Jamani suna da shiri na kawo cibiyoyin sana’ar dogora da kai, kuma akwai kamfanoninsu da suke da sha’awar kafa hanyoyin koyar da sana’a. kasan ba wai sai wanda ya yi karatu bane kawai zai samu aikin yi don haka wannan zai samar da ragowar masu kaura zuwa Jamani”. In ji sabon Jakadar
Da yake jawabi a kan wakilcin da zai yi wa Nijeriya a kasar Jamus kuwa, Ambasadan ya shaida cewar “Jamus kasa ce mai matukar muhimmanci, tana kuma kan gaba a yankin kasashen Turai. ”Duk da cewa jahohinsu bai kai namu ba, amma babbar kasace, Jamus tana da jahohi 16 ne, sai dai manya ne kuma sun jima suna samun ci gaba ta fuskacin kimiyya, cinikaiyya, kere-kere da kuma ilimi. Sannan sun kasance wacce take da tsohon dangantaka da Nijeriya” in ji shi.