Connect with us

SIYASA

Zan Shawo Kan Matsalar Yunwa Da Fatara A Nijeriya, Tambuwal

Published

on

A shekaranjiya ne, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, wanda yanzu haka gwamnan jihar Sakkwato ne, ya sha alwashin cewar muddin ya zama shugaban kasar Nijeriya zai yi kokarin shawo kan matsalar yunwa da fatara da suka addabi kasar nan ta Nijeriya a halin yanzu.

Tambuwal wanda ke neman jam’iyyar PDP ta tsaida shi neman wannan kujerar, ya shaida hakan ne a Bauchi a lokacin da yake ganawa da wakilan jam’iyyar PDP a sakatariyarsu da ke Bauchi a ranar Alhamis din nan.

Ya kara da cewa, kwarewarsa da saninsa kan hidimar mulki kasantuwarsa wanda ya shafe shekaru a matsayin Kakakin majalisar tarayya, kuma masani kan harkokin shari’a yana da ilimin sanin yadda za a tafiyar da kasar nan ba tare da fuskantar matsaloli a tsakanin ‘yan majalisu da bangaren gwamnati ba, yana mai shaida cewar zai kuma yi kokarin gyara matsalolin da gwamnatin APC ta rigaya ta lalata.

Tambuwal ya shaida cewar ya bar jam’iyyar APC ne domin muradinsa na kyautata Nijeriya da kuma maida kasar, kasa mai cike da ci gaba, don haka ne ya bayyana halin da Nijeriya take ciki a yau a matsayin wani yanayi mai cike da kalubale ta fuskacin tsaro, rashin zaman lafiya, talauci, yunwa da fatara, inda ya tabbatar da cewar zai yi kokarin samar da tsaro, lafiya, shawo kan tattalin arzikin kasar nan da sauran muhimman aiyukan da ya ce in aka zabeshi zai yi su.

Ya ce; “kowani dan Nijeriya na kukan yunwa da matsalar fatara. Yara da dama suna cikin yunwa, mutane da dama suna kukan babu da sauran musifun da suka yi wa Nijeriya katutu. Mutane da dama sun gaza samun nagartaccen rayuwa, suna rayuwa cikin mawuyacin hali, a yanzu haka ‘yan Nijeriya da dama suna rayuwa cikin yunwa da fatara,”

“Domin shawo kan irin wadannan matsalolin da suke jibge, suna daga cikin dalilan da suka sanya na amsa kiranyen da tulin matasan kasar nen ke min na in fito neman shugabancin kasar Nijeriya,” Inji gwamnan sokoto

Waziri Tambuwal ya nemi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP su tsaida shi domin ya samu nasarar cimma mudinsa na kyautata Nijeriya, “Don haka ina rokonku idan an zo zabe ku zabemu domin mu samu nasarar cimma muradinmu na gyara kasar nan. za mu yi amfani da gogewarmu da kwarewarmu wajen yin kyakkyawar shugabanci ba tare da nuna son kai ko shigar da bangaranci ba, ina tabbatar muku zan yi kokarin aiki mai kyau, ba zan watsa muku kasa a ido ba muddin kuka zabeni,” A cewar shi Tambuwal

Gwamnan Sokoton ya yi amfani da yaba wa Kakakin majalisar tarayya na yanzu Yakubu Dogara a bisa tabbatar da samar da hukumar inganta shiyyar Arewa Maso Gabas wanda majalisar ta yi da zimmar farfado da shiyar daga nan kuma ya yi kira na mwusamman ga shugaban kasar Nijeriya, Alhajin Muhammadu Buhari dangane da hanzarta sanya hanu kan wannan dokar domin fara aiki da shi, “Yan majalisu sun yi kokarin samar da wannan hukumar amma yanzu kusan wata tara shugaban kasa ya ki sanya hanu kan wannan dokar, don haka ina kira a garesa ya sanya hanu kan wannan dokar ko kuma mu idan muka zo mu sanya hanu kan dokar,” Inji Tambuwal

Da yake maida jawabinsa, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Akuyam ya tabbatar da cewar jam’iyyar PDP za tta yi tsayuwar daka wajen fitar da nagartacce dan takarar da zai iya kaisu ga nasara, ya yi albishin wa Tambuwal da cewar masu ruwa da tsaki na PDP a jihar Bauchi za su tabbatar da zaban wanda ya dace a lokacin zaben fidda gwani.
Advertisement

labarai