Zan So Koma Wa Amurka Da Buga Wasa, Cewar Messi

Sevilla

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya ce yana da burin wata rana ya buga wasa a kasar Amurka, amma ya ce bashi da tabbacin abin da zai faru nan gaba idan kwantiraginsa ya kare a watan Yunin shekara mai zuwa.

Messi, dan kasar Argentina, mai shekara 33 a duniya, zai iya fara ciniki da kungiyoyin da suke bibiyarsa na kasashen ketare a watan Janairu banda wadanda suke a kasar Sipaniya kamar yadda dokar hukumar kwallon kafa ta duniya ta tsara.

Ce-ce-ku-ce kan makomar Messi a nan gaba ya karu matuka tun bayan da Messi din ya nemi barin kungiyar a watan Agustan wannan shekarar sai dai daga baya tsohon shugaban kungiyar ya hana dan wasan tafiya inda yace dole sai an biya Barcelona yuro miliyan 700 idan anaso a dauki shahararren dan wasan duniyar.

“Ban san me zan yi ba tukuna a halin yanzu saboda ba Magana bace wadda mutum zai yanke hukunci lokaci daya ko kuma wadda zai yanke shi kadai akwai bukatar tattaunawa da abokan shawara” in ji Messi a wata hira da yayi a tashar talabijin ta La Sedta ta Sifaniya.

Ya ci gaba da cewa “Zan jira sai karshen kakar wasa amma kuma ina so na buga wasa a kasar Amurka domin sanin ya rayuwa take a can da kuma sanin yadda League yake a can, amma kuma zan dawo Barcelona da sauran karfi na”

Messi ya kara da cewa “A yanzu, abu mafi muhimmanci shi ne na mayar da hankali kan Barcelona na kammala wannan kakar da kyau, da kuma mayar da hankali wurin cin kofuna kada wani abu ya dauke min hankali”.

Barcelona, wadda ba ta ci kofi a kakar da ta gabata ba, ita ce ta biyar a La Liga bayan sun yi wasa mafi muni a farkon gasar cikin shekara 33 kuma a kwanakin baya Messi da kansa ya bayyana cewa dalilin da yasa baya kokari a wannan kakar ya samo asaline da rashin bashi dama yabar Barcelona.

Tun bayan da Messi ya shiga Barcelona lokacin yana da shekara 13 a duniya, Messi ya zama wanda ya fi zama zakara a tarihin kungiyar ta vangaren cin kwallaye, inda ya ci gasar La Liga 10, da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League sau hudu da kuma lambar yabo ta Ballon d’Or sau shida – wadda lambar yabo ce da ake bawa dan wasan kwallon kafa da ya fi shahara a duniya duk shekara.

Yunkurin da ya yi a kwanakin baya na barin Barcelona ya ci karo da ra’ayin shugaban kungiyar na wancan lokaci, Josep Maria Bartomeu, wanda ya sauka a watan Oktoba sannan daga baya Messi ya alakanta saukar Bartommeu a matsayin “bala’i”.

“Wannan wani yanayi ne mai wuya ga Barcelona, amma wadanda ke cikin kungiyar sun san yana cikin mawuyacin hali, abubuwa sun lalace kuma yana da wahala Barcelona ta koma yadda take a baya,” a cewar Messi a kwanakin baya.

Tuni dai aka fara alakanta Messi da komawa wasu daga cikin manyan kungiyoyi a duniya ciki kuwa har da Manchester City ta Ingila wadda mai koyarwa Pep Guardiola yake koyarwa kuma Messi sunyi aiki da Guardiola a lokacin zamansu a Barcelona na tsawon sehkara hudu.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tana daya daga cikin kungiyoyin da suke bibiyar dan wasan inda ko a kwanakin baya dan wasa Neymar na kungiyar sai da ya bayyana cewa zai iya barin PSG din idan basu sayo masa Messi ba a karshen kakar wasa ta bana.

Bugu da kari shugabannin kungiyar kwallon kafa ta PSG suna ganin idan suka dauki Messi ya koma kungiyar zasu samu damar ci gaba da rike Neymar sannan shima matashin dan wasa Mbappe zai iya zama idan har yaga Messi ya koma kungiyar.

A kwanakin baya ne Mbappe ya sanar da shugabannin kungiyar cewa zai iya barin kungiyar a karshen kakar wasa inda tuni kungiyoyin Juventus da Real Madrid da Liverpool suka fara nuna sha’awarsu ta ganin sun dauki Mbappe, dan Faransa.

Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi a cikin watan Janairu domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.

Exit mobile version