Santurakin Kagara" />

Zan Tabbatar Mutum Dubu Sun Yi Rajistar APC A Mazabata – Santurakin Kagara

Santurakin Kagara

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Neja, Malam Ibrahim Balarabe ( Santurakin Kagara) ya sha alwashin ganin mutum dubu daya sun karbi sabon rajistan jam’iyyar APC a mazabarsa ta cikin gari a mazabarsa ta akwatin zaben maikatifa. Santuraki ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin godiya ganin yadda ya tarba daga mutanen Kagara a lokacin da ya tafi sabunta rajistansa na zama cikakken dan jam’iyya.

Santurakin ya cigaba da cewar da wanda ya shiga jam’iyyar APC yau, da wanda aka kafa jam’iyyar tare da shi a baya duk matsayin su daya a cikin jam’iyyar nan muddin ya karbi wannan rajistan, saboda haka ina shawartar duk wani mai son cigaban dimukuraddiya da karamar hukumar Rafi ya gaggauta karban wannan rajistan domin APC ce jam’iyyar da ta yarda da tafiya akan tafarkin dimukuraddiya wanda hakan zai taimaka wajen cigaban siyasar kasar nan.

Maganar bambamce-bambance a jam’iyyar APC a karamar hukumar Rafi ba gaskiya ba ne, domin duk wani mai fada a ji a karamar hukumar nan da ke cikin jam’iyyar nan kan mu hade yake, kuma tare muke yiwa al’ummar mu aiki.

A wannan tawagar yau ga tsohon shugaban karamar hukumar Rafi, Hon. Gambo Tanko Kagara, wanda shi ne babban mai baiwa gwamna shawara akan harkokin kananan hukumomi da masarautu, ga kuma babban daraktan hukumar agajin gaggawa ta jiha, da sauran mukarraban gwamnatin jiha da ta karamar hukumar Rafi duk a wannan wajen.

Babu wani abu da zai taso a karamar hukumar nan, muddin aka sanar da mu ba mu hadu muka dauki mataki akan sa ba, matsalar tsaro abu ne da ya shafi kowa kuma gwamnatin jiha na bakin kokarinta akai wanda a kowani lokaci idan akwai abinda yafi damun maigwamna Abubakar Sani Bello bai wuce maganar tsaro ba.

Saboda haka masu yayata cewar gwamnati ba ta komai, mutane ne masu matakan da gwamnati ke dauka zagon kasa, amma shi kan shi maigirma hakimin Tegina shugaban majalisar hakiman kasar Kagara muna aika da shi kafada da kafada akan maganar tsaro a karamar hukumar nan.

Duk masu fakewa da matsalar tsaro suna yiwa kasar Kagara zagon kasa, muna addu’ar Allah ya tona asirinsu ya karya su, domin duk wanda yace bai son zaman lafiya, bai son cigaban masarautar nan da jihar nan mu ma ba masoyin mu ba ne.

A na shi jawabin, tsohon shugaban karamar hukumar Rafi, kuma tsohon shugaban kungiyar ALGON ta kasa, Hon. Gambo Tanko Kagara, yace zuwan gwamnatin Abubakar Sani Bello karamar hukumar Rafi ta anfana, an samar da abubuwan cigaban karamar hukumar da dama.

Kamar yadda Santurakin Kagara ya fada ne a baya kan mu daya ne kuma tare muke aikiwa karamar hukumar nan, maganar rarrabuwar kawuna ba gaskiya ba, idan ma suna yada wannan batu na rarrabuwar kawuna zuwan mu a wannan wajen yau ya nunawa jama’a cewar daman ba gaskiya suke fada ba, ina kira da babban murya ga mutanen Rafi kowa ya fito dan marawa jam’iyyar APC baya akan kudurin sabunta rajistan zabe.

Alhaji Ibrahim Kaga, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jiha, yace lokaci yayi da za mu kara jawo hankalin jama’ar mu wajen cigaba da baiwa gwamnati goyon baya musamman na ganin ta cin ma muradunta wajen kawo karshen rashin zaman lafiya a jihar, domin babu jiha ko karamar hukumar da za ta bunkasa ta cigaba muddin babu zaman lafiya.

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin kwamitin sabunta rajistar jam’iyyar a mataki na kasa, bisa jagorancin Alhaji Yusuf Abubakar Egun da wasu daga cikin shugabannin rikon jam’iyyar a mataki na jiha.

Exit mobile version