Dan wasa Martin Odegard wanda ya koma Arsenal daga Real Madrid ya bayyana cewa zai yi iya kokarinsa wajen taimakawa kungiyar wajen samun tikitin gasar cin Kofin Zakarun Turai na Champions League na kakar wasa mai zuwa.
dan wasan mai shekara 22 a duniya dan kasar Norway bai samu lokacin buga wa Real Madrid wasanni sosai ba a karkashin kociyan kungiyar Zinedine Zidane a kakar bana wanda hakan yasa ya nemi tafiya zaman aro domin ci gaba da samun buga wasanni.
kungiyoyin Real Sociedad da Ajad suma sun nuna sha’awar su ta daukar Odegard wanda ya buga wasannin aro a baya a Soceidad din sai dai tuni Arsenal ta cimma yarjejeniya da Real Madrid na daukar dan kwallon da take sa ran kila ya buga mata wasa da Manchester United ranar Asabar.
Wani masannin harkokin wasanni dan kasar Sipaniya, Guillem Balague ya ce Real Madrid ta zabi dan kwallon ya je buga gasar Premier League maimakon Real Sociedad domin zaifi samun irin gogewar da suke bukata.
Kuma zai je Arsenal bayan da Mesut Ozil ya koma Fenerbahce da buga gasar Turkiya wanda aka kai ruwa rana kafin cinikin wanda ya kawo karshen zaman shekara bakwai da rabi da Ozil yayi yana bugawa kungiyar wasa.
Odegard ya koma Real Madrid daga Stromgodset a watan Janairun shekara ta 2015 ya kuma buga wa Real Madrid wasa tara a kakar bana sannan Real Madrid tana ta biyu a teburin Laliga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Atletico Madrid mai kwantan wasa daya ita kuwa Arsenal tana ta 11 a teburin Premier League da maki 29, bayan buga karawa 19.