Connect with us

LABARAI

Zan Taimaka Wa Gwamnan Bauchi Da Dukkanin Karfina -Abdu Katagum

Published

on

A Jiya Litinin ne aka rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Arc. Abdu Sule Katagum, inda jiga-jigai daga gwamnatin APC a jihar Bauchi suka hallara a dakin taro na Multipurpose domin shaida wannan amsar rantsuwa kama aikin.
Tun da fari, Alkalin Alkalai ‘Grand Khadi’ na jihar Bauchi Dahiru Abubakar Ningi shi ne ya jagoranci mika wa sabon mataimakin rantsuwar kama aiki a matsayin mataimakin gwamna, daga cikin ababen da ya karantu masa na doka, ya yi alkawarin tafiyar da aiki bisa doka da oda ba tare da shigar da son rai na kashin kai a yayin aiki ba.
Bayan da ya kammala karantu masa ka’idoji da dokokin kasancewa a wannan mukamin, inda shi kuma Katagum ya amince da dukkaninsu, nan take ya mika masa rantsuwar kasancewa a matsayin mataimakin gwamna.
Da yake jawabinsa na godiya, sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Arc. Abdu Sule Katagum ya sha alwashin taimaka wa gwamnan jihar da dukkanin karfinsa, yana mai bayanin cewar zai yi amfani da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu wajen kyautata shugabanci da tafiyar da harkokin gwamnati yadda ya dace a jihar ta Bauchi.
Ta bakinsa; “Na fi shekara 40 muna tare da gwamna, tun muna yara muke tare, cikin ikon Allah bamu taba samun wata sabani a tsakaninmu ba.
“Ina son na tabbatar wa gwamna wani abu; ban da kasancewarka abokina, kai dan uwana ne. kuma wannan gwamnatin taka, duk abun da za mu yi ko wanda zan yi domin na taimaka maka da rike maka amana zan yi,” In ji Abdu Katagum.
Katagum ya kuma sha alwashin yin duk mai iyuwa wajen kyautata shugabanci a jihar ta Bauchi, “Mutanen Bauchi ina son na tabbatar maku yanzu za a samo aiki, yanzu muka soma aiki domin ci gaban jihar nan cikin yardar Allah. Za mu sake neman jama’a mu zauna da jama’a domin sake maida gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin gwamnan Bauchi,” In ji sabon mataimakin gwamnan jihar.
Daga bisani ya gode wa gwamnan jihar ta Bauchi a bisa zabinsa da yayi hade da mika masa wannan babban kujerar, haka kuma, ya gode wa mai dakinsa Hajiya Mariya Abdu Sule Katagum inda ya bayyana cewar da gudunmawarta ne ya samu nasarar tattaka matakan da ya hau kawo yanzu.
Katagum, ya kuma nuna gayar godiyarsa da jinjinsa wa majalisar dokokin jihar Bauchi, inda ya bayyana cewar da yunkurinsu ne wannan lamarin ya tabbata, baya ga nan, ya kuma gode wa dukkanin manyan Sarukuna iyayen kasa a bisa tsoma tasu gudunmawa wajen samun wannan nasarar.
Da yake tasa jawabi a wajen amsar rantsuwar, gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana cewar zabin Katagum a matsayin mai mukami na biyu a Bauchi na zuwa ne a sakamakon zaman da suka yi da masu ruwa da tsaki dangane da zabin wanda zai maye gurbin tsohon mataimakinsa da ya ajiye aikinsa a kashin kansa.
Ya ke cewa; “Na zauna na nutsu wajen zaben nagartaccen mutumin da zai maye wannan gurbin, mun zauna da masu ruwa da tsaki a jihar ne domin tabbatar da yin zabin da ya kamata; daga karshe dai Abdu Sule Katagum ya kasance zababben wadanda muka zaba domin ya rike wannan babbar kujera mafi daraja ta biyu a jiha.
“Ina fatan zamu hada hanu waje guda domin tabbatar da kyautata rayuwar jama’an jihar Bauchi, hade da girmama darajar jihar,” A cewar GMA.
Abubakar, ya kuma kara da cewa, “Ina kuma kira ga dukkanin sassa da rassan gwamnatin jihar nan da su tabbatar da baiwa Abdu Katagum hadin kai domin ya samu nasarar sauke nauyin da ke kansa, Allah kuma ya bashi ikon sauke nauyin da muka daura masa,” In ji Gwamna M.A
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya kara wa jihar Bauchi zaman lafiya da ci gaba, inda ya nemi sabon mataimakinsa ya yi aiki da doka da ka’idojin da suke a akwai don kyautata aiki.
Gabanin a kai ga rantsar da Sule Katagum a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bauchi, an karanta wa illahirin mahalarta taron takaitaccen tarihin sabon mataimakin gwamnan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: