Zan Taimakawa Kano Pillars Ta Koma Ta Farko A Gasar Firimiya – Ahmad Musa

Pillars

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmad Musa, ya bayyana cewa zai taimakawa kungiyar ta Kano Pillars domin ganin ta koma mataki na daya a gasar firmiyar Nigeriya.

A daren ranar Alhamis ne dai kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kaddamar da dan wasan a gaban magoya baya inda kuma dan wasan ya nuna farin cikinsa ga wannan mataki daya daukarwa kansa na sake dawowa tsohuwar kungiyarsa.

Tun a satin daya gabata ne dai aka fara rade radin cewa tsohon dan wasan na CSKA Moscow zai dawo Kano Pillars duk da cewa kungiyar kwallon kafa ta Plateau United itama tayi zawarcin dan wasan.

“Zan yi iya yina wajen ganin na taimakawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars saboda haka na dawo wannan kungiya ne saboda ina kaunar ta kuma daga nan na fara saboda haka kamar gida na dawo” in ji Ahmad Musa

Ya ci gaba da cewa “Zan taimakawa wannan kungiya domin ganin mun kai mataki na daya akan teburin gasar Firimiya kuma ina fatan zan samu hadin kai a wajen shugabanni da ‘yan wasa domin ganin mun kai kungiyar ga nasara”

Shima a nasa bangaren, kociyan tawagar Super Eagles ta Nijeriya Gernot Rohr ya yi amanna cewa, dan wasansa Ahmed Musa zai samu cikakken horo a gasar firimiyar kasar nan kafin a fara gasar cin kofin nahiyar Afrika a farkon shekara mai zuwa.

Kalamansa na zuwa ne bayan Kaften Din na Super Eagles ya koma tsohuwar Kungiyarsa ta Kano Pillars domin ci gaba da buga wasa sannan ya taya dan wasan farin cikin ci gaba da bugawa tsohuwar kungiyarsa wasa.

Rohr ya ce, ya yi matukar farin ciki da dan wasan ya koma Kano Pillars saboda kungiyar na da kwarewa sannan kuma yana fatan dan wasan zaiyi amfani da damar da ya samu domin kara kwarewa.

Kocin ya sha caccaka a lokacin da ya gayyaci Musa domin buga wa Najeriya wasanta da Benin da kuma Lesotho a gasar neman girbin shiga gasar cin kofin Afrika a karshen watan daya gabata.

Kafin kulla yarjejeniya da Kano Pillars, dan wasan ya share tsawon watanni yana zaune ba tare da wata kungiya ba tun bayan da ya raba gari da kungiyar Al-Nesyri ta Saudiya a cikin watan Oktoban shekarar bara.

Exit mobile version