Zan Wakilci Argentina A Kofin Duniya – Messi

Kofin Duniya

Dan wasan tawagar kasar Argentina, Leonel Messi, ya bayyana cewa ba zaiyi ritaya daga bugawa kasar wasa ba kuma zai wakilci kasar a gasar cin kofin duniyar da za’a buga a shekara mai zuwa.

A ranar Asabar Messi ya lashe kofinsa na farko a da tawagar kwallon kafar kasarsa bayan da kwallo daya tilo da Angel Di Maria ya saka a raga ta bawa Argentina nasara 1-0 a kan masu masaukin baki Brazil a wasan karshe na gasar cin kofin Copa America da ya gudana ranar Asabar.

Wannan nasarar a filin wasa na Maracana a Rio de Janneiro na kasar Brazil ta kawo karshen zama na shekaru 28 babu wani babban kofi da Argentina ta yi, sannan ta kawo karshen kwanaki dubu biyu da dari 5 da Brazil ta yi ba a doke ta a gida ba.

Rabon Argentina da lashe wata babbar gasa tun a  shekarar 1993, lokacin da kwallaye biyu da shahararren dan wasanta Gabriel Batistuta ya ci suka ba ta nasara a kan Medico a  wasan karshe na Copa America a kasar Ecuador.

Kuma ya yin da Messi  mai shekaru 34 ya kawo karshen rashin lashe babban kofi a kasarsa, Neymar dan kasar Brazil, wanda ya ke kasa da Messi da shekaru 5 ba shi da wani babban kofi da ya lashe da tawagar kasarsa, bayan da Brazil ta lashe kofin babu shi, shekaru biyu da suka wuce saboda raunin da ya samu.

Publicité

Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid da Benfica, Di Maria, ya ci wa kasar  Argentina kwallonta ne a minti na 22 da fara wasan, kuma ita ta makale har aka tashi daga wasan.

Exit mobile version