Zan Warke Daga Cutar Korona -Muhammad Salah

Klopp

Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasan tawagar kasar Masar kuma na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah, ya bayyana cewa babu wata damuwa a tattare dashi kuma nan gaba kadan zai warke daga cutar Korona wadda ta kamashi a ranar Juma’ar data wuce.

Dan wasan na Liverpool Mohamed Salah, gwaji ne ya tabbatar da yana dauke da cutar ta korona yayin da ya tafi bugawa kasarsa ta Masar wasa kuma hukumar kwallon Masar ce ta tabbatar a ranar Juma’a cewa Salah mai shekara 28, sakamakon gwajin korona da aka yi masa ya nuna yana dauke da cutar.

Sai dai hukumar ta ce sauran ‘yan wasan kasar gwaji ya nuna cewa ba sa dauke da korona kuma zasu ci gaba da bugawa tawagar kasar wasa kamar yadda aka tsara kuma Masar ta karbi bakuncin tawagar ‘yan wasan kasar Togo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika a jiya Asabar.

Yanzu Salah zai killace kansa kuma zai kauracewa buga wa Liverpool wasanni na tsawon mako biyu duk da cewa a ranar Asabar mai zuwa Liverpool za ta karbi bakuncin Leicester City a Premier League kafin ta hadu da Atalanta a filin wasa na Anfield a gasar zakarun Turai.

Dan wasa Salah a bana ya buga wa Liverpool dukkanin wasanninta a Premier inda ya ci kwallaye takwas sia dai rashin dan wasan a wannan lokacin ba karamar barazana bace ga Liverpool din wadda take fama da rashin ‘yan wasan baya sakamakon ciwon da sukeji.

Exit mobile version