Zan Yi Iya Kokarina Wajen Kawo Cigaba A Ajingi – Hon. Murtala Baiye

Ajingi

Daga Bala Kukkuru,

Shugaban karamar hukumar Ajingi ta Jihar Kano, Hon. Murtala Uba Dam Baiye a jingi ya bayyana cewa, zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya kawo ci gaban ga a karamar hukumar a jingi da ke wayenta a cikin jihar kano.

Shugaban karamar hukumar ta a jingi honarabul murtala uba dam baiye a jingi ya yi wannan ta’alikin ne a gidansa da ke garin a jingi a lokacin da yake karbar bakuncin wadansu matasa da sauran ‘yan siyasar shi na yankin garin a jingi da suka zo masa gaisuwar ban girma tare da tayashi murnar samun nasarar lashe zaben karamar hukumar a jingi da kewayanta wanda ya gudana a wancan lokacin a cikin daya daga cikin kananan hukumomi guda arba’in da hudu da ake da su a cikin jihar kano, kuma ya samu nasarar lashe zaben karamar hukumarsa ta a jingi a yayin da ya cigaba da nuna wa matasa da sauran al’umma farin cikinsa a game da wannan ziyara da suka kawo masa, inda ya cyake cewa, babu shakka yana mai nuna farin cikinsa tare da godiya ga matasa da sauran al’ummar karamar hukumar a jingi a game da wannan ziyara da suka kawo masa.

Ya kara da cewa, kuma zai yi iyakar kokarin sa wajen ganin ya kawo cigaba a karamar hukumar ta a jingi da kewayanta da al’ummar da ke cikinta baki daya sannan kuma ya cigaba da cewa, haka zalika ya ke Isar da sakon godiya ga Gwamnatin jihar kano a karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi umar ganduje, a kokarinsa na kawo abubuwan ci gaban jihar kano da dana zaman lafiya, wanda a cewarsa, wannan nema ya sanya suka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar ta kano guda arba’in da hudu cikin kwanciyar hankali a duk fadin jihar.

Ya ci gaba da cewa, yana isar da sakonsa na godiya ga Iyayen siyasar shi ta karamar hukumar a jingi da kewayanta, musamman wadanda suka sanya hannuwa da bakunan su wajen tabbatar da shi a matsayin Shugaban karamar hukumar a jingi da sauran matasan yankin, yana yiwa kowa da kowa fatan Alheri da fatan Allah uban giji ya saka masu da Alheri.

Kuma Ya ci gaba da cewa, yana mai shawartar matasan karamar hukumar a jingi, jihar kano da Nijeriya baki daya da su ci gaba da bayar da tasu gudummawar a wajen kawo al’amurran da za su ci gaba da kawo zaman lafiya a jihar kano da Nijeriya baki daya, da fatan Allah uban giji ya cigaba da zaunar da kasar nan lafiya da kwanciyar hankali baki daya.

A karshe ya jinjinwa kwamishinan kananan hukumomin jihar kano Alhaji murtala sulan Garo da shugaban jam’iyar APC na jihar kano, Alhaji Abdullahi Abbas bisa kokarin da suka yi na tabbatar da kawo ci gaban jihar baki daya.

Exit mobile version