Gwamnatin tarayya ta ce kiraye-kirayen da ake na Shugaban Kasa Buhari da ya yi murabus kan kisan kiyashin da Boko Haram ta yiwa manoman shinkafa a garin Zabarmari na jihar Borno maganar teburin mai shayi ce kawai.
Ministan watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da ‘ya’yan kungiyar masu buga jaridu ta Nijeriya (NIPAN) da yammacin yau Alhamis a birnin Legas, a cewarshi wannan kiran ba komi bane illa siyasa da wasu suke yi da lamarin tsaro.
Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya (NAN) ne ya ruwaito wannan maganar, a cewar Lai Muhammad; daga jin rahotannin kisan, sai ga masu kiraye-kiraye suna bukatar Shugaban Kasa da ya yi murabus, daga jin wannan kiran kasan ana so ne a siyasantar da batun tsaron kasa, wanda ba komi bane illa maganar kawai.
“An zabi Shugaban Kasa ne a shekarar 2015 don yin wa’adin shekarun hudu, sannan aka sake zabar shi a shekarar 2019 don saki yin wasu shekaru hudun, don haka babu wata maganar banza da za ta hana shi karasa shekarunshi hudu a kan Mulki.” Inji Lai Muhammad