Zanen Dake Cike Da Bayanan Batun Auduga

Daga CRI Hausa

A baya-bayan ne kamfanonin H&M da Nike da sauran wasu kamfanonin sayar da tufafi na kasa da kasa suka yada suka tare da neman a kauracewa audugar jihar Xinjiang ta kasar Sin. Da safiyar ranar 27 ga wata ne kuma, mai zanen barkwanci na Cartoon, Wuhe Qilin, ya fitar da wani sabon zane a shafinsa na sada zumunta, wanda ya kunshi batun auduga, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin masu amfani da internet. Zanen da aka yi wa taken “blood cotton initiative” ya nuna yadda wani gungun manema labarai da ‘yan sanda masu sanye da fararen hula fuskokinsu rufe, suke zantawa da wani mutum-mutumi a gonar auduga, yayin da a bayansu kuma, akwai wasu bayi bakaken fata dake aiki tukuru suna tsinkar auduga.
A wannan zane, akwai batutuwa da dama masu ban sha’awa. Kimanin sa’o’i 2 bayan wallafa shi, ya samu jinjina daga daruruwan dubban mutane.
Zanen, wanda aka yi wa taken “blood cotton initiative” ko BCI a takaice, ya yi daidai da taken “better cotton initiative” wato tsarin kyautata samar da auduga, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da martani ga sukar da ake wa audugar jihar Xinjiang. “better” wanda ke nufin kyautatawa, ya maye gurbin “blood” wato jini, a matsayin sabuwar ma’anar BCI, wanda ya bayyana makircin kungiyoyin kasashen yamma.
Kugiyar da uban gidan bayin ya yi amfani da ita wajen gwada nauyin auduga a zanen, ta yi kama sosai da tambarin kamfanin Nike. Sannan a bayan bakin bawan, akwai jan kalmomin “HM”, wadanda ke nufin “help Me” wato “a taimake ni”.
A cikin hoton, akwai bakin bawa dauke da bulala. Wannan shi ne asalin rayuwar da bayi bakaken fata suka yi.
Dukkan bayin dake cikin hoton na sanye ne da fararen hula masu tsini. Wannan tambari ne na kungiyar 3k, dake rajin daukaka fararen fata da nuna wariyar launi.
A can kasa ta hannun daman hoton, dan sandan da ya duka ya yi kama da dan sandan Amurka da ya danne wani bakar fata da gwiwa har ya mutu.
Sannan, manema labaran kasashen yamma, sun yi biris da mutanen dake rataye a kan bishiya da bayin da ake musgunawa, inda suke hira da mutum-mutumin dake sanye da rawani. An maye hannun mutum-mutumin na hagu da hannun wanke jini. A lokaci guda kuma, wani bawa bakar fata na tsaye a bayansa, hannun bawan daya a yanke. Masu amfani da shafin intanet sun bayyana lamarin a matsayin irin karyar da dan Adam kan shirga, haka zalika, mai tayar da hankali.(Mai fassarawa: Faeza Mustapha daga CRI Hausa)

Exit mobile version