Zanga-zanga: Minista Ya Nemi Jama’a Su Ƙara Haƙuri, Gwamnati Na Ƙoƙarin Rage Tsadar Rayuwa 
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zanga-zanga: Minista Ya Nemi Jama’a Su Ƙara Haƙuri, Gwamnati Na Ƙoƙarin Rage Tsadar Rayuwa 

bySulaiman
1 year ago
Amurka

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman matasa masu shirin zanga-zanga, da su yi haƙuri.

A halin yanzu wasu ‘yan Nijeriya na ta yin shelar cewa, za su yi zanga-zangar lumana a ƙarshen wannan watan domin bayyana ɓacin ransu kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.

  • Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Don Tantancewa
  • Abokan Kasuwancinmu Na Zuwa A Kai-A Kai Don Neman Man Da Muke Tacewa – Dangote 

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Asabar, ministan ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wasu muhimman matakai domin magance matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

Ya ce: “Akwai mataki na farko da gwamnati ta ɗauka na a samu a raba kayan abinci ga al’ummar Nijeriya. An kai shinkafa jihohi duka ga baki ɗaya talatin da shida da kuma yankin Abuja.”

Ya ƙara da cewa, “Akwai wani shiri da ake yi na CNG, ma’ana wannan harka na iskar gas wanda duk motocin da za su yi aiki, za su yi aiki da wannan na’ura, wato ta iskar gas, misali idan kana kashe naira goma wajen sufuri yanzu kuɗin ka zai dawo ƙasa ma da naira huɗu. Ka ga an sake samun cigaba.

“In ka lura da abin da ake yi kamar na bututun gas na AKK wanda kwanakin baya an je Kaduna an sake duba shi, ya kai kusan wato kashi casa’in da biyar da gamawa. Abu ne da aka fara tun waccan gwamnatin da ta shuɗe.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kuma ya tsaya tsayin daka lallai a samu a gama wannan shiri saboda idan aka yi shi za a samu sauƙi sosai.

“Duk kamfanonin da aka rurrufe saboda matsalar wutar lantarki da ɗimbin al’umma da suka rasa ayyukan su saboda rufe kamfanunnuka idan Allah ya yarda za su dawo.”

Ministan ya yi nuni da cewa Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da Shirin Lamunin Ɗalibai don ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi su samu damar zuwa makaranta.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma ƙaddamar da harkar wato abin da ake ce ma Student Loan, wato bashi saboda a yi makaranta. Yana takaicin cewa bai kamata a ce wani yaro bai iya zuwa makaranta ba saboda iyayen sa ba su da kuɗin biya masa makaranta.

“Yanzu duk wani wanda ya iya cin jarabawa, duk wani yaro ɗan Nijeriya, cikakken ɗan Nijeriya da ya iya cin jarabawa, zai iya zuwa ya amfana a biya masa bashi mai sauƙi cikin rahusa ya biya kuɗin makaranta, ba ma kawai a biya kuɗin makaranta ba, ya samu kuɗin da kuma zai iya ɓatarwa har ya gama karatun sa.”

Dangane da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta duk da alƙawurran da Shugaba Tinubu ya yi na kawo sauƙin rayuwa, Idris ya ce: “Lallai gwamnati ta yarda cewa akwai wannan matsatsi. Abin da ya bambanta gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatoci da yawa shi ne idan akwai matsala akan amsa a ce lallai akwai matsala a wuri kaza amma kuma ga abin da mu ke yi na a samo maslaha.

“A yanzu maganar da ake yi a harkar tsaro abin da muke ciki misali shekara ɗaya baya, ko shekara biyu baya, ai ka ga abin ba haka ba ne.

“Mu na fata a haɗa ƙarfi da ƙarfe, su mutanen ƙasa su ba gwamnati goyon baya domin a kawo ƙarshen wannan al’amari.

“Saboda haka a ƙara yin haƙuri, kiran da gwamnati ke yi kenan. A ƙara yi wa gwamnati haƙuri, idan Allah ya yarda a hankali a hankali za a kawo ƙarshen wannan al’amari.”

Ministan ya ce akwai tanadi da gwamnati ta yi wa manoma inda Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta hanyar Ma’aikatar Aikin Gona, ya raba taki buhu miliyan dubu ɗari ɗaya da hamsin ga manoma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
Wang Yi: PLO Ita Ce Kadai Halatacciyar Wakiliyar Al’ummar Falasdinu

Wang Yi: PLO Ita Ce Kadai Halatacciyar Wakiliyar Al’ummar Falasdinu

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version