Ibrahim Ibrahim" />

Zanga-zangar EndSARS: Hadakar CNG Ta Fara Tattara Alkaluman Asarar Da ‘Yan Arewa Suka Yi A Kudu

Dakta Buhari

A ci gaba da ziyarar jaje da ta’aziya da Hadakar Shugabanin Kungiyoyin Arewa wanda a turance ake kira da Coalition of Northern Groups (CNG), ta kai ziyara na musamman ga Al’ummar Arewa Mazauna Jihar Ribas, domin jajanta masu da kuma hada alkaluma na irin ta’adi da barna ta dukiyoyi da rayuka da aka yi a yayin rikicn zanga-zangar EndSARS, da ya gudana a kwanakin baya.

 

A lokacin ziyarar da Hadakar kungiyoyin Arewa suka kai, sun sami ganawa da Sarakunan Arewa Mazauna yankin, da sauran Al’umar Arewa mazauna yankin na kudu, sannan sun sami ganawa da Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyemson Wike.

 

Tun da farko a yayin nasa jawabin a Fadar Mai martaba Sarkin Hausawa Mazauna Jihar Ribas, Shugaban Hadakar Kungiyoyin Arewa, Alhaji Nastura Ashir Shariff, ya bayyana ma Sarkin Hausawa cewa, sun yanke kawo wannan ziyara ne domin su jajanta masu da kuma yi masu ta’aziya abisa abin alhinin da ya afka masu a yayin gudanar da zanga zangar Endsars wanda ya gudana a kwanakin baya.

 

Shugaban Hadakar kungiyoyin Arewa, ya kuma kara da bayyana cewa, a yayin wannan ziyara da suka kawo wannan yanki na kudancin kasar nan, zasu yi amfani da wannan dama domin ganin sun sami asalin adadin kididdiga asarar rayuka da na dukiyoyin ‘yan Arewa da suka salwanta.

 

Nastura Ashir Shariff, ya ci gaba da bayyana cewa, da zarar sun kammala wannan ziyarar gani da ido da suka kawo, zasu mika rahoton su ga Shugaban Gwamnonin Arewa, domin ganin sun yi tsayin daka a gwamnatance an dauki nauyin biyansu diyyar asarar rayuka da na dukiyoyin da suka yi, kamar yadda suma takwarorinsu na sauran yankunan kasar nan za’ayi masu.

 

Sannan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohin kudancin kasar nan, da suyi duk mai yuwuwa wajen ganin suna kare rayuka da dukiyoyin Al’ummar ‘Yan Arewa Mazauna yankin kudancin kasar nan. Domin a cewarsa, ba zasu ci gaba da zura ido suna kallon wasu batagari na azabtar da Al’ummarsu a wasu sassa na yankunan kasar nan ba.

 

Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Hausawa Mazauna Fatakwal, Alhaji Isa Madaki JP, ya bayyana jin dadinsu da wannan ziyara da Shugabanin Hadakar kungiyoyin Arewa da suka kawo masu, sannan ya bayyana masu irin zamantakewar dake tsakaninsu da sauran kabilu Mazauna Jihar Ribas.

 

Sarkin Hausawan Mazauna Jihar Ribas, ya kara da bayyana cewa, yana mamakin irin kalaman da wasu Al’ummar kasar nan keyi na cewa, ya kamata a raba kasar nan, a cewarsa, raba kasar nan ba abin wasa ba ne, domin ba’a raba kasa a yayin zama irin na teburin Mai shayi.

 

Sarkin Hausawan ya kuma fito fili karara ya bayyana masu cewa, maganar gaskiya shi ne, ita fa Gwamnatin Tarayya da na jihohi,  kansu da na dukiyoyinsu kawai suke tsarewa, amma babu abin da ya damesu da tsare rayuka da dukiyoyin Al’ummar da suke shugabanta.

 

Shima a nasa jawabin a yayin da yake amsar ziyarar da tawagar Hadakar Shugabanin kungiyoyin Arewa suka kawo masa, Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyemson Wike, ya bayyana masu cewa a matsayinsa na Gwamnan Jihar Ribas, jiharsa a bude take ga duk wani Dan yankin kasar nan da zai zo kasuwanci ko aiki a wannan jiha, matukar zai kiyaye dokokin da Gwamnatin jihar ta shimfida masa.

 

Gwamna Wike, ya kara da bayyana cewa, tun kamin Gwamnatin Tarayya ta haramta ayyukan ‘yan kungiyar fafutukar yankin biyafura, shi tuni Gwamnatinsa ta riga ta haramta ayyukan ‘yan kungiyar a duk fadin jihar baki daya. A cewarsa, abin da ya faru a yayin zanga zangar Endsars, babu hannun gwamnati jihar a ciki lamarin, sannan ya sake fitowa fili ya yi Allah waddai da abin da ya faru, na rasa rayuka da dukiyoyin Al’umma. Sannan ya yi alkawarin bayar da tallafi ga wadanda suka rasa rayuka da dukiyoyinsu a yayin zanga zangar. A cewarsa.

Exit mobile version