Ibrahim Ibrahim" />

Zanga Zangar EndSARS: Matasan Arewa Sun Soki Lamirin Kungiyar Amnesty

Kungiyar Amnesty

Gamayyar kungiyoyin Matasan Arewa 19 sun soki lamirin kungiyar nan mai rajin kare hakkin Dan Adam ta Amnesty  bisa ga kwarmaton da take ta yi akan Harbe-Harben Lekki tare da kawar da kai akan matsalar tsaro da yankin Arewa ke fama da shi.

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira a Gidan Tarihi na Arewa dake kaduna, domin mayar da martani dangane da wata takarda da Shugaban kungiyar Amnesty Mista Osai Ojigho, ya fitar ya na mai kalubalantar Gwamnatin Tarayya da yunkurin rufe gaskiyar abin da ya faru a Lekki.

Mai magana da yawun kungiyoyin Matasan Abdul-Azeez Suleiman ya ce, abin mamaki ne da takaici yadda kungiyar Amnesty ke kokarin nuna bambanci a ayyukan kungiyar ta kokarin fifita wasu da mantawa da wasu.

Matasan sun koma nuna damuwar su akan matakan da kungiyar Amnesty ta dauka hadda shugaban ‘yan Sanda na kasa ta hanyar bada fifiko ga Zanga-Zangar Endsars ta Kudu da fatali da Endinsecurty ta Arewa.

A cewarsu, “Ya kamata a gane cewar Zanga-Zangar Endsars an faro ta ne a cikin watan Oktoba daga yankin Kudancin Nijeriya, suna bukatar a soke rundunar SARS, amma Zanga-Zangar Endinsecurty an an faro ta ne wata hudu da suka gabata, suna nuna damuwa da halin tsaro ya ke shiga Arewa”.

Bisa ga haka gamayyar kungiyoyin suna kira ga kungiyar Amnesty da ta farka daga barcin da take ciki ta fuskanci abubuwan da ke addabar kasar nan, amma ba wani yanki na daban ba.

Sannan sun kalubalanci Amnesty da ta fadada ayyukan da take hankoron yi zuwa ga yankin Arewacin Nijeriya, inda ya dade yana fama da matsaloli na tabarbarewar tsaro.

“Mu na kuma gayyatar kungiyar Amnesty da ta ziyarci yankin Arewacin Nijeriya ba sashin kudancin kasar nan ba kadai, sannan ta kasance mai gudanar da bincike ba nazari da dogaro da labaran kanzon kurege ba. Domin batun kashe Kashen Lekki ko Gwamnatin Jihar Legas ta musanta faruwar hakan”.

Daga karshe Matasan na Arewa sun tunatar da kungiyar ta Amnesty cewa, mutuncin su zai kasance ne kawai ga jama’a, idan ya zamana suna adalci akan ayyukan su. A cewar Gamayyar Kungiyoyin Matasan.

Exit mobile version