Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ya bada umarni na cewa a gaggauta sakin masu zanga-zanga mutum 35 da aka kama yayain zanga-zangar #OcupyLekkiTollgate.
Su dai masu zanga-zangar sun shiga hannun ‘yan sanda ne a ranar Asabar lokacin da suka yi kokarin fara gudanar gudanar da wani sabon zanga-zanga da suke kalubalantar sake bude hada-hada kamar da baya a Lekki Toll Plaza, wanda aka rufe biyo bayan zanga-zangar kin jinin jami’an SARS a kwanakin baya cikin watan Oktoban 2020.
Idan za ku iya tunawa dai a makwan jiya an samu cacar baka a tsakanin gwamnati da masu zanga-zangar, inda jami’an tsaro suka ce babu wanda ya isa ya fito gudanar da zanga-zanga a Toll Gate jiya Asabar, har ma suka ce shege ka fasa. A yayin da su kuma masu zanga-zangar suka ce atafau babu gudu ba ja da baya sai sun fito zanga-zanga domin bayyana bukatarsu.
Umarnin sake masu zanga-zangar da aka cafke da kwamishinan ‘yan sandan Legas ya bayar na zuwa ne bayan da Lauyoyi biyu, Oladotun Hassan da Ayo Ademiluyi, suka bukaci a sake masu zanga-zangar da aka kama, tare da neman a tabbatar da cewa hakkin mutunta dan adam da rashin keta wa dan adam haddinsu babu wanda aka karya daga cikin dokokin kiyaye mutuncin dan adam.
Suka ce, “Mun yi Allah wadai da matakin da jami’a n ‘yan sandan RRS da LSST suka nuna wajen cafke masu zanga-zangar lumana.”
Sun kuma zargi ‘yan sandan da kokarin tauye hakkin jama’a na bayyana ra’ayi da fito da abun da ke damunsu a bayyanar jama’a.