Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Zantukan Hikima

by
9 months ago
in NAZARI
3 min read
Hikima
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Idris Aliyu Daudawa

Kada ka wulakanta na kasa, domin kana ganin kai ka taka sama sannu a hankali za kai mamaki lokacin dawowarka kasa, domin kana iya haduwa da shi yana kuma iya taimaka maka domin al’amarin Allah haka yake.

Shi al’amarin duniya kudusun ne kuma fana’unne shi ya sa ana iya ganin wani yana tare da kudusun yayin da wani kuma yana tare fana’un, wannan ba wani abin yi illa sai dai a rungumi kaddara.

Labarai Masu Nasaba

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

Duk inda huntu za shi, sai da sanin mairiga hakanan ma shi huntu ko an ki sa ran biki ranar gini a neme sa. Kada dai kaza ta yi murna domin ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta, wani tsuntsu yana gudun ruwa amma agwagwa a ciki take kwana

Kowa ka gani da tabarmarsa sai dai ya rasa wurin shimfidawa,mai kaza a aljihu baya jimirin as-as, duniya juyi-juyi ce kwado ya fa  ruwan dumi, kada dai zomon gida ya kashe Karen masu gida. Samu ya fi iyawa hawan dokin dan maciji,wanda ruwa ya ci idan ya ga takobi sai ya kama.

Idan damina taki mutum ganyen makani sai ya yanke shi, abinda rowan dumi ya dafa idan aka yi hakuri na sanyin ma dafawa zai yi, fara koyon mulki da baki kafin ka iya da hannu, Idan wuta ta kone mutum da ya ga toka sai ya dage kafarsa, idan tsari yayi tsami sai Akuya mai gemu

Sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba, ya ya za a yi mai zazzabi ya ci mara? duk inda yaro ya tsinci wuri can yakan fi saurin tunawa, daga sannu Sarkin fawa sai miya ta kama zaki, duk inda ruwa ya je ya dawo to kwari za ya.

Ya za ai na sayar da Jaka ta dawo tana gugar man danga, sai da ruwan ciki akan ja na rijiya,duk wanda ya samu lamuni ga dodo shiga ruwa ba wani abu bane, akwai ranar kin dillanci ranar da rigar maigari za ta bata.

Wanda bai fita ruwa ba baya matse warki, maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi gumi. Kada dai a bari har wankin hula ya kai dare, ba a yabon dan kuturu sai ya shekara hamsin da yatsu.

Daga kallon gada sai kurtuku ya dahe mani, dama ai mutum tara yake bai cika goma ba, a yi kokari a fidda jaki daga cikin duma, ba a fafe gora ranar tafiya, mahakurci mawadaci, da safe ake kame fari idan rana ta yi sai su tashi.

Mai tarko ba ya taka kara, kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, mai ido daya baya gode Allah sai ya ga makaho, abin aljihu duk na mairiga ne, ai ana wata hakama in ji gwanin rawa daya fadi, ban yi tsammanin farin goro zai yi tsutsa ba amma dana bara sai ga maciji.

Kyan dinyar makaho ta nuna aljihunsa, ba a fafe gora ranar tafiya,  idan mace ta ce miji Babanta ne sai ya mutu bai yi mata gara ba, icen darni shi ko gida dama a baya yake, ba, aba Biri ruwa keda wuya ba, yadda za a dauko kwanon bayan ya gama sha. Kyawun da ya gaji ubansa, da ruwan ciki akan ja na rijiya, zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayinsa

Babu ruwan Biri da gada saboda ai tsallakewa yake, kowa ya kona rumbunsa ya san inda toka take kudi, ba samun duniyar ba inda za aci in ji dan tsako. Sai an kada gizo sannan ace koki ta taso, mai bayarwa yana wata wandada watarana shi za a bashi, Yau da gobe bata bar komai ba, ita kuma ce mai sa a mari amarya, kada kuma kallon hadari yasa ayi wanka da kashi, domin ba a sani ba watakila shi hadarin ba ruwa zai yi ba.

Ko  an ki budurwa da aure dole ne watarana a ganta da goyon danta, tusa ko ruwa aka yi ta warinta sai ya fito  waje, za a iya tilastawa doki ya je rafi ne kawai, amma ba shan ruwa ba, duk karya ne ake tusa bata hura wuta, sai wani karon kuma Bera ya barad da jikon Mage, a ture baya raba Kare da Kura, kada dai ayi shuka kan idon Makwarwa.

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Nijeriyar Jiya!

Next Post

Mene Ne Hukunce-Hukuncen Mai Takaba?

Labarai Masu Nasaba

Dariye Da Nyame

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
4 weeks ago
0

...

Bangaranci

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

by Muhammad Maitela
2 months ago
0

...

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

by
3 months ago
0

...

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by
7 months ago
0

...

Next Post
Takaba

Mene Ne Hukunce-Hukuncen Mai Takaba?

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: