Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Zaratan Jami’an NIS Sun Cafke Wani Dan Kamaru Da Haramtattun Fasfuna

Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ke sintirin tsaron iyakar kasa a yankin Yala na Jihar Kuros Riba, sun cafke wani Dan Kamaru da ya karya dokar da gwamnatin tarayya ta sanya ta hana kai-komo a tsakanin kasa da kasa domin dakile bazuwar cutar Korona.

Da yake yi wa shugaban NIS na kasa, CGI Muhammad Babandede MFR bayani a kan lamarin, Kwanturolar hukumar mai kula da Jihar Kuros Riba, Okey Ezugwu ya bayyana cewa, Dan Kamarun mai suna Kouaha Diedonne, mai shekaru 42 a duniya, an cafke shi ne dauke da fasfuna na kasashe daban-daban da ba mallakarsa ba. Daga ciki akwai fasfo guda biyu na Kamaru da Kasar Gini-Bisau dauke da sunansa da kuma wasu fasfo guda biyar na Nijeriya mallakar wasu mutane daban.

Shugaban na NIS, Babandede ya umurci a gudanar da kwakkwaran bincike a kan kamen tare da gabatar da rahoto a kai, kana ya yaba wa Kwanturolar Kuros Riba da jami’an da ke aikin tsaron iyaka a Yala bisa kyakkyawan aikin da suka yi cikin kwarewa tare da yin biris da tayin karbar cin-hanci wajen cafke mutumin.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labaru na NIS, DCI Sunday James ta yi karin hasken cewa za a gurfanar da mutumin domin hukunta da shi daidai da laifinsa a karkashin dokar shige da fice.

 

Exit mobile version