El-Zaharadeen Umar" />

Zargin Almundahana: Kotu Ta Tura Tsohon Gwaman Katsina Ibrahim Sheme Gidan Yari

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Babbar kotun tarayya da ke Katsina ta bada umarnin tsare tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shehu Shema bisa zargin yin almundahana da kudadan SURE-P har Naira miliyan dubu biyar da miliyan dari bakwai

Ita dai wannan kara hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wata EFCC ce ta shigar a gaban kotun inda suke zargin tsohon gwamnan ya yi kuruciyar bera da wadannan kudade a lokacin da yake kan mulki wanda suka ce laifin hadin baki ne da cin amana da kokarin maida dukiyar jama’a tasa.

Tun a shekaranjiya litinin ne aka fara sauraran wannan kara a baban kotun tarayya da ke Katsina, inda aka tafka muhawara tsakanin lauyoyin bangarorin guda biyu sannan daga karshe aka dage sauraran karar zuwa jiya talata domin cigaba da karar.

Tun da farko lauyan hukumar EFCC  Lateef Fagbemi (SAN) ya shaidawa babar kotun cewa wannan kara ce da ake zargin tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema ya yi burda ciki da kudadan SURE-P a lokacin da yake akan mulki saboda haka suna bukatar kotu ta saurari karar domin yin hukunci.

Sai da kuma a nashi bangaran lauyan da ke kare wanda ake kara, Emmanual Ukala (SAN) ya kalubalanci hurumin babbar kotun inda ya bayyana cewa baban Atoni Janar na kasa ne kadai yake da hurumin gabatar da wani mutun a gaban kotu kuma ya bada iznin wani ya gabatar a madadinsa saboda haka kadda wannan kotun ta sauarani wannan kara  saboda bata da hurumin yin hakan.

An dauki dogon lokacin ana kiki-kaka a tsakanin lauyoyin guda biyu a ya yin da na EFCC yake da’awar cewa suna da hurumin gabatar da wanda ake zargi a gaban kuton, shi kuma lauyan na Shema yana cewa ba su da wannan hurumi kuma kowa yana kawo na shi dalili da hujjuji daga wasu shari’o’I da suka gabata.

Bayan daukar dogon lokaci ana tafka muhawara a ranar litinin sai alkalin babar kuton tarayya da ke Katsina, Babagana Ashigar ya bada hutu domin duba da kuma nazari game da wannan muhawara da lauyoyi suka tafka tare da bada hukuncin kotu.

Bayan dawowa daga hutan da kuto ta bada, sai alkali Babagana Ashigar ya bada hukuncin cewa wannan kotun tana da hurumin sauraran wannan karar kamar yadda dokar kasa ta bada ya kuma kawo hujjujinsa game da hukunci da ya bada..

Daga nan sai lauyan hukumar EFCC Lateef Fagbemi (SAN) ya nemi kuto da ta bada iznin wanda ake zargi ya shi akwatin tuhuma domin a karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa game da wannan karar da suka shigar, anan ne kuma lauyan Shema Emmanual Ukala (SAN) ya ce ina, ai ba a zo wajan da haka zata faru ba, kamar dai bai amince da hurumin kotun ba, sai dai ya kara da cewa wanda ake tuhuma (tsohon gwamna Shema) ya zo kuto ba bisa gayyata ba, saboda acewarsa ba a ba su takardar sammaci ba, sun zo ne domin girmama kotu.

Akan wadannan batutuwa sai da aka dauki dogon lokacin anan tafka muhawara har zuwa karfe biyar na marece, inda daga karshe alkalin baban kotun tarayya da ke Katsina Babagana Ashigar ya dage sauraran karar zuwa jiya talata domin bada hukucin kotu game da muhawara da aka tafka na cewar wanda ake zargin bai kamata ya shiga akwatin tuhuma ba domin a karanta masa tuhumar da ake yi masa.

A jiya talata an sa cewa karfe tara na safe za a fara zaman sai daga baya aka  maida karfe biyu na rana domin cigaba da sauraran karar. Bayan an dawo kuma kowane bangare sun halarci kotun, sai alkali ya zauna ya fara bada hukuncin muhawarar da aka tafka a shekaranjiya game da jayayyar da ke akwai akan cewa Shema ya shiga akwatin tuhuma domin a karanta masa tuhumar da ake yi masa

Kotu ta bada hukuncin cewa wanda ake tuhuma tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema ya shiga akwatin tuhuma domin a karanta masa tuhumar da ake yi masa ta yin kasa da fadi da tsabar kudi har naira biliyan biyar da miliyan dari bakwai na SURE-P

Daga nan sai alkalin kotun ya bada umarnin cewa wanda ake zargin zai iya shiga akwatin tuhuma domin karanta masa tuhumar da ake yi masa, haka kuma aka yi ya shiga aka karanta masa tuhuma 26 inda nan take kotu ta tambayeshi ko ya fahimci karar da ake yi masa? ya ce ya fahimta, amma dai wannan zargin da ake yi masa ba haka bane, ya musanta.

Daga cikin tuhume-tuhume 26 da aka karanta masa sun hada da cewa kai Ibrahim Shehu Shema a lokacin da kake gwamnan Katsina a ranar 16 ga watan maris, 2015  a Katsina cikin hurumin  wannan kotu ka bada umarnin  cire kudi miliyan 575 kudin SURE-P  daga bankin Fidility da ke Katsina domin yin shirin tallafawa matasa amma baka yi hakan ba, wannan laifine da ya sabawa sashe na 15 (2) (d) na dokar satar kudadai ta 2011 kuma ana yin hukunci a karkashin sashi na 15 (2) na wannan dokar.

Bayan kammala karanto tuhume-tuhume 26 wanda tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema ya ce ya fahimci tuhumar sai dai ba haka bane, sai lauyansa ya nema a ba wanda ake tuhuma beli, inda nan ma wata sabuwa muhawara ta sake barkewa tsakanin lauyoyin guda biyu inda lauyan EFCC ya dage kai da fata cewa ba su yarda a bada Shema beli ba saboda wasu dalilai da ya bayyanawa kotu shima lauyan Sheman ya nema a bada belin wanda yake karewa tare da bada na shi hujjujin.

Bayan daukar dogon lokaci ana tafka wannan muhawara sai alkali ya bada ba’asin kotu inda ya bada umarni a tsare wanda ake tuhuma a wajan ajiyar mutane da ke karkashin kulawar hukumar EFCC da ke Kano har zuwa ranar 27 ga wannann watan da muke ciki domin duba yadda za a bayar da belin wanda ake zargin tare da sa ranar da za a fara gabatar da shaidu domin cigaba da wannan kara.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai jami’an hukumar EFCC sun tisa keyar tsohon gwamnan zuwa jihar Kano domin cigaba da tsare shi har zuwa ranar juma’a inda za a dawo aji abinda kuto zata ce game da wannan shari’a da ka yi wa lakabi da mace mai ciki…

Idan za a iya tunawa hukumar ta EFCC tana tuhumar tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema tare da wasu mutane uku a gaban babar kotun jiha ta 3 bisa zargin yi kasa da fadi da kudadan kananan hukumomi a lokacin da yake akan mulkin da suka kai naira biliyan goma sha daya.

Ya zuwa yanzu an sa ranar 30 da kuma 31 ga watan mayu 2018 domin cigaba da sauranara karar da ake zargin Shema da mutane uku a gaban babbar kotun jiha ta 3 sai kuma ga wannan sabuwa

Exit mobile version