Connect with us

LABARAI

Zargin Badakala: Fadar Shugaban Kasa Ta Wanke Abba Kyari

Published

on

A shekaran jiya Asabar ne fadar Shugaban kasa ta bara kan zargin aikata badakalar kwangila da ake yi wa Shugaban ma’aikatan fadar ta Shugaban kasa, Abba Kyari.
Abba Kyari ya ce, zai dauki matakan shari’a a kan wanda ya dora masa wannan zargin na badakalar sama da fadi da kuma matakin Shari’a a kan Jaridar Punch.
An yayata zargin badakalar kwangilan ne a wani gidan rediyo mai suna, ‘Berekete Family Radio 101.1FM, da ke Abuja.
Wani mai suna, Bako Kyari ne ya bayyana a gidan Rediyon na, Berekete Family Radio 101.1FM, Abuja, wanda ya ce shi dan’uwan shugaban ma’aikatan ne na fadar ta shugaban kasa, Abba Kyari, da kuma wani mai suna Sani Ado, wanda ya yi zargin yana aiki ne da hukumar BPP, wanda kuma ya karbi Naira milyan 29.9 daga hannun sa da sunan zai sama masa wani aikin kwangila.
Bako ya ce, ya rubuta takardan koke ga hukumar EFCC, amma sai hukumar ta ki ta yi wani abu a kai, kamar kuma yanda ya yi zargin yanda hukumar ta EFCC ta kama shi tare da tsare shi na makwanni biyu.
Amma a cikin sakon da Abba Kyarin ya aike wa tashar talabijin ta Cable, ya yi rantsuwan daukan matakin shari’a a kan wanda ya lakaba masa wannan zargin, wanda ya ce, ba kamshin gaskiya a cikin sa.
“Na umurci Lauyoyi na da su shirya kai karan duk wadanda aka kulla wannan sharrin tare da su.
“Sam ba kamshin gaskiya a wannan maganan. Ba za mu bar wasu tsiraru su kitsa wani abin da babu gaskiya a cikin sa ba.
A cikin sanarwan da Kakakin Shugaban kasan, Garba Shehu ya fitar, fadar Shugaban kasan ta mayar da martani ga Jaridar ta Punch, wacce ta yi hira da Bako din kuma ta yayata hirar.
“Fadar shugaban kasa, ta dauki wani labari da aka buga a ranar Asabar, wanda ya yi magana a kan wani zargin neman cin mutunci a kan mai taimaka wa Shugaban kasa, Abba Kyari a matsayin babban laifi, inda aka zarge shi da karban cin hancin Naira milyan 29 domin ya bayar da kwangila.
“A nan muna bayyana wa bisa tabbaci cewa, sam wannan zargin ba gaskiya ne ba, shi kuma Shugaban ma’aikatan na fadar ta Shugaban kasa, bai taba yin wani zama shi da wanda yake yin wannan zargin ba.
“Abin mamakin ma shi ne, yadda Jaridar ta Punch ta amince da buga hirar duk da yadda labarin da ake bayarwa a cikin hirar ke cike da lankwashe-lankwashe, kamar ta inda hukumar ta BPP ta karyata cewa, shi tushen mai bayar da labarin, sam ba ma’aikacin ta ne ba. Kasantuwar mawuyacin halin babban zaben da ke tafe, wasu ‘yan siyasa da kafafen yada labarai suna ta dada kaimin ganin sun lakaba wa gwamnatin Shugaba Buhari, wani zargin zubar da mutunci mara asali.
“Mun kuma yi la’akari da cewa, babu batun wata kwangilar sayo motocin Hilud guda 15 ga fadar ta shugaban kasa, ba ma kwangila ce da aka bayar ba, domin ba inda hakan ya nu na a kasafin kudin fadar ta shugaban kasa na shekarar 2016 da 2017.
“Mun duba kasafin kudin fadar na 2016 da 2017, sam ba wannan maganan. Ta ya kuwa Abba Kyari zai nemi a ba shi kudin kwangilar da sam ba ta?
“Bayan hakan, kudin ma da ake zargin an bayar a matsayin cin hanci, su ma abin dubawa ne, domin a baya an san yadda a duk wata ake bayar da Naira milyan 200 ga wannan ofishin ba kuma tare da wani ya ce, me aka yi da su ba.
“A lokacin da Abba Kyari ya shiga wannan ofishin ne kadai ya dakatar da hakan.
“A gaskiya, yana da wahala a yi zargin an bayar da cin hancin Naira milyan 29 ga jami’in da ya guji Naira milyan 200 a duk wata, wadanda babu mai tambayar sa abin da ya yi da su.
“Muna kara janyo hankalin manema labarai a kan su guji yada duk wani zargi a kan jami’an gwamnati da ba a tatance su ba a hukumance, ba kuma da bin ka’idar aikin jarida ba.
“Mun sanar da jaridar ta Punch, wurare da daman da karyar wannan labarin ke bayyana, amma duk da hakan sai suka ci gaba suka wallafa wannan raunannan zargin . don haka sai su shirya tarban Abba Kyari a kotu,” in ji Garba Shehu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: