Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Zargin Badala: Mai Gidan Abincin Da El-Rufai Ya Rushe Za Ta Kotu

by Khalid Idris Doya
January 5, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Rushe Gidan Abinci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mai mallakin gidan cin abincin nan na ‘Asher Kings and kueens Restaurant’ da ke Kaduna, Misis Aisha Mercy Yakubu, ta sha alwashin garzaya wa kotu, domin neman hakkinta bisa rushe ma ta muhallinta.

Babban wurin cin abincin da aka rushe a makon jiya, wanda hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta dauki alhakin yi bisa zargin shirya wani bikin badala na rawar jima’i, lamarin wanda ya yadu a kafafen sadarwar zamani da har hakan ya sanya gwamnatin jihar daukar matakin rushe wajen.
A sanarwar da Misis Aisha Yakubu ta fitar a jiya Litinin, Aisha wacce matar Kakakin jam’iyyar adawa ta PDP ce ta jihar, Abraham Catoh, ta shaida cewar, wani bari daga cikin wurin an bada hayarsa domin sayar da abinci, ta ce, an yi wa muhallin rijistar (CAC) da wurin sayar da abinci da kuma wurin taro, amma ba otel ba ne.
Ta ce, sun hango babbar mota tare da ’yan sanda dauke da bindigogi, inda suka rushe wajen.
“Na tambayi shugaban tawagar, don jin meye makasudin hakan, ya ki kula ni, sai ya ce min zai yi min bayani ne kawai idan na je caji ofis din Sabon Tasha,” in ji shi.
Ta ce, an rushe wajen ne da zargin ana shirya tarukan badala wacce ita kuma ta ce ba dalilin haka suke bada hayar wajen ba, ta shaida cewar wurin taro ne suke bayar amma ba su da masaniyar ga abun da wasu za su je su yi.
Yakubu ta yi zargin cewa ta biya Naira 100,000 na belin wani ma’aikacinta da ’yan sanda suka kama.
Aisha ta kuma ce, an rushe dukkanin muhallin wajen ba tare da sanar da ita ba kafin hakan.
Ta kara da cewa, firgicin wannan lamarin ya jawo mata barin cikinta na wata daya sakamakon jin labarin da ya firgitata.
“Ina kan shirye-shiryen daukan matakin shari’a bisa rusa min muhallina,” a cewarta.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Tattalin Arziki: Da Alama 2021 Za Ta Yi Wa Nijeriya Kyau – CBN

Next Post

Matsalolin Tsaro Na Kara Ta’azzara A Yankin Birnin Gwari, Inji BEPU

RelatedPosts

Marayu

’Yan Bindiga Sun Sace Marayu Bakwai A Gidan A Marayun Abuja

by Khalid Idris Doya
1 hour ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Akwai dan dsoro na alamun tashin...

Bogi Wiwi

Legas: An Cafke Dan Sandan Bogi Da Wiwi

by Khalid Idris Doya
1 hour ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Rahotanni daga Jihar Legas, sun zo...

Aguda

Mutum Ya Rasu A Arangamar Matasan Unguwar Aguda Dake Surulere

by Khalid Idris Doya
1 hour ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, An tabbatar da mutuwar mutum daya...

Next Post
Garkuwa

Matsalolin Tsaro Na Kara Ta’azzara A Yankin Birnin Gwari, Inji BEPU

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version