Zargin Bata Suna: Osinbajo Ya Maka Mutum Biyu A Kotu

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya maka wasu mutum biyu a kotu, bisa zargin bata masa suna da yake zargin sun yi.

A shafinsa na Facebook, Farfesa Osinbajo ya wallafa cewa; ‘A ‘yan kwanakin nan da suka gabata, wasu tsirarun mutane sun yi ta yada karerayi a kaina a kafafen watsa labarai.’

A yau na shigar da mutanen biyu kara kotu wadanda su ne suke yada wadannan karerayi. Inji Osinbajo

Ya kara da cewa; Zan kawar da duk wata rigar kariya da tsarin mulki ya ba ni domin ganin an bi min hakkina dangane da bata min suna da yi min karya da aka yi.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da zargin da tsohon mataimakin sakataren watsa labaran jam’iyyar APC, ya yi, yayin wata hira da wata kafar watsa labarai, cewa hukumar tattara haraji ta kasar, FIRS, ta bai wa mataimakin shugaban kasar biliyoyin naira domin yin kamfe a zaben 2019.

Mutanenk sun yi zargin cewa batun kudin da FIRS ta bai wa mataimakin shugaban ne ya janyo rashin jituwa tsakanin Osinbajo da wasu mukarraban gwamnati a fadar shugaban kasa.

Exit mobile version