Connect with us

LABARAI

Zargin Cin Hanci: Kotu Ta Hana Shekarau Zuwa Umrah

Published

on

Mai shari’a Zainab Abubakar, ta babbar Kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Kano ta ki amincewa da bukatar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya gabatar mata a ranar Talata na ba shi fasfo dinsa domin ya sami sararin tafiya aikin Umrah a kasar Saudi Arabiyya.

Shekarau ya isa kotun ce a ranar 28 ga watan Mayu da bukatar na shi na a ba shi fasfo din na shi domin ya tafi kasar ta Saudiyya domin yin aikin Umrah, daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 23 ga watan Yuni 2018.

A martanin da ya bayar kan wannan bukatar, Johnson Ojogbane, ya yi amfani da sashe na tara ne wajen sukan wannan bukatar.

A lokacin da aka kira shari’ar ranar Talata, Lauyan da ke kare Shekarau din. Abdul Adamu, nan take ya mika bukatar na su a rubuce.

Shi kuma lauyan da ke gabatar da karar, Mista Ojogbane, ya gabatar da na shi takardun sukar mai sakin layi tara. Inda ya bukaci kotun da kar ta amince da bukatar.

Da take yanke hukunci alkaliyar kotun cewa ta yi, “Bisa la’akari da hujjojin da mai kare wanda ake kara ya gabatar da kuma na mai gabatar da karan, ina ganin ba bukatar sakin fasfo din wanda ake karan domin rike fasfo din na shi yana daya daga cikin sharuddan bayar da belin na shi.

Don haka sai ta yi watsi da bukatar ta sakin fasfo din sabili da rashin hujja mai karfi kan hakan.

Hukumar EFCC ce dai ta gabatar da Shekarau din a kotun tare da wasu mutane biyu, Aminu Wali da wani mai suna,  Mansur Ahmed, bisa tuhumar su da ake da hadin bakin karbar Naira milyan 950,000,000 daga cikin dala milyan115,000,000, wanda ake zargin tsohuwar Ministan albarkatun Mai, Deizani Alison-Madueke, da yin watandan su domin yin magudi a zaben 2015.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: