Zargin Cin Zarafi: Gaskiyar Halin Da Ake Ciki A Gidan Yarin Goron Dutse
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Cin Zarafi: Gaskiyar Halin Da Ake Ciki A Gidan Yarin Goron Dutse

byShehu Yahaya
5 months ago
Dutse

Biyo bayan zargin yin lalata da maza a gidan gyaran hali dake Goron Dutse a jihar Kano, hakunta hukumar kula da gidajen ta jihar Kano ta musanta zargin inda tace zargin bashi da tushe ballantana makama.

A wata ziyara da wakilunmu ya Kai gidan yarin domin ganewa idonsa da kuma binciken abinda ke faruwa bisa zargin cewa ana lalata maza.

A yayin ziyarar wakilinmu ya Shiga dakunan daurarrun da dakin kallon Talabijin da dakin shan magani harda coci da masallaci da kuma ganin irin  abincin da ake basu a  kowacce rana , harma da kulawar da ake basu idan basu da lafiya tare da tantance abunda da suka gani dangane da zargin da ake yi.

  • Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A Kano
  • An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano

Zargin Wanda ya tayar da hankalin iyayen da ‘ya’yansu ke zaman gidan kurkuku. Lamarin da ya haifar da cunkoso a gidan yarin wajen kawo ziyara ga fursunonin. Alkaluma sun Bayyana Cewa a kullum gidan yarin  oron Dutse yana samu makuncin masu ziyara sama da guda dubu daya domin ganewa idanunsu halin da yaransu da ‘yan uwa suke ciki a gidan.

Leadership Hausa ta samu damar zantawa da wasu fursunonin inda suka tabbatar da cewa ba a aikata abunda ake zargi ba.

Binciken leadership Hausa ya tababatar da cewa daga ranar 6 ga watan mayun shekarar 2025 jimmilar fursunonin da suke zaune a gidan gyaran Hali na Goron sun Kai 1,950 daga cikinsu akwai guda 1, 551 masu jiran shari’a sai guda daya yana kwance a asibiti wadanda kashi cas’in cikin dari na fursunonin matasa ne wadanda basu wuce shekaru 25 zuwa 40 ba. Emmanuel Nmandi dan asalin jihar Imo Wanda Kuma shine shuban dakin (cell 8) Wanda akewa lakabi da dogon daki yace ya shigo gidan gyaran halin tun shekarar 2020 wata shekararsa biyar kenan amma bai taba sanin akwai wani lokaci da ake lalata da maza ba.

Shi dai dogon daki shine gini mafi dadewa a gidan  wanda gini na wasa wanda Kuma a dakin ne  ake zargin ana lalata da fursunonin.

Ya ce iya zamansu a gidan ba suga wurin da ake aikata hakan ba, kuma basu taba samun labari makamancin haka ba kawai karyace da aka shiryawa hukumar gidan yarin.

Sai dai wani abun burgewa a kowanne daki da fursunonin suke zama akwai sufeto janar da ‘yan sanda da kwamishina ‘yan sanda da mataimakinsa da da Alkali haka akwai jami’i mai kula ban daki wadanda suke aiki duk bayan awa uku-uku dare da rana domin kaucewa aikata badala a dakunansu.

Shima Bashir Dan mama kofar Na’isa wanda aka yankewa hukucin zaman gidan gyaran Hali na iya rayuwa ya ce “ Yau Shekarata Goma sha shidda Ina zama a wannan gida wanda duk wani da aka ganshj a gidannan a idona ya shigo zan rantse maka da Allah irin tarbiyyar da aka samu a gidan kurkuku tafi wacce aka samu a gidajenmu Saboda mu da muke a gidan mune muke baiwa kanmu tarbiyya domin gyara halinmu.

“ A iya sanina babu wani fursuna da ya iya ya aikata badala a cikin wannan gidan muna kallonsa wai har ta Kai ga ana aikata luwadi. Wai tayaya ma haka za ta faru domin mu da kanmu muna da masu zirga zirga babu dare babu rana. Hatta idan irin wadanda suke kwana a kan tabarma mutum ya jefawa na kusa da shi kafa yayin da yake barci shi mai kula da dakin baya sanya hannu ya cire masa kafa sai da ya sanya sanda ya tasheshi domin ya gyara kwanciyarsa. Alal misali masu shiga dakin wanka ko bahaya mai kula da dakin shike raba lambar shiga dakin bahaya ko wanda ba zaka shiga ba sai ka nuna lambarka Wanda babu ta yadda mutum biyu zasu shiga tare”

“Rayuwar a gidan kurkuku Abar koyi saboda duk lokacin da iyayemu suka kawo mana ziyara suna Jin dadin yadda suke ganinmu sai dai kawai ace Bama cikinsu.

“Batun zargin luwadi babu gaskiya mu da muke cikin gidan mune zamu tabbatar da zargin” inji shi.

Sai dai fursunonin sun bakaci mahukutan gidan yari da Su kara dagewa wajen kara inganta abincin da suke ci da kula da lafiyarsu domin sau da yawa Idan aka samu matsalar rashin jini ga fursunonin jamian gidan suke karokaro na jini wajen tallafawa marasa lafiya.

Sun bayyana cewa duk da cewa suna cin abinci Amma bada koshi yafe kawai suke yi inda suka ce akwai bukatar a karo musu yawan abincin da ake dafa musu Kwanan baya wani Shehu Adamu, ya yi zargin cewa ana lalata da maza a gidan yarin Goron Dutse, kuma hakan ya sanya mutane sama da 200 basa iya zama har tsutsotsi suke fitowa daga mazaunansu.

Matashin yace yayi zama a gidan yarin har na tsawon shekaru tara, lamarin da ya haifar cece kuce a fadin kasar nan.

Sai dai Kakakin hukumar kula da gidajen gyara ta jihar Kano Musbahu Lawan, yace karyata zargin inda yace  matashin bai taba zama a gidan yarin Goron Dutse ba , amma ya taba zama a gidan yarin Kurmawa, kuma watanni hudu kachal ya yi, ba kamar yadda ya bayyana ba cewa ya shafe shekaru 9 a gidan ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan fitar wani sautin murya da aka yada a shafukan sada zumunta, inda matashin mai suna Shehu Adamu, ya yi zargin cewa ana lalata maza a gidan yarin Goron Dutse.

An jiyo matshin na cewa ‘’ a halin da ake ciki daman dai neman maza a kurku munsan tsohon laifi ne, to amma abunda yake faruwa kamar a kirashi da fyade, tunda ana amfani da raunin dan adam ta hanyar a bashi Magi Dunkuli, garin kwaki a hannu to ana amfani da wannan abubuwa na lalata yara musamman yan shekara 18, 19 da 20 ta hanyar neman, wasu ma yanzu basa iya zama saboda nemansu da ake yi ta baya wanda takai a yanzu akwai sama da mutane sama da 200 wadanda basa iya zama da bayansu saboda tsutsotsi ne suke fitowa ta bayansu.

Matashi Shehu Adamu, da ya bayyana kansa a matsayin Na’ibin limamin masallacin gidan gyaran hali na Goron Dutse a jihar Kano,Tunda fari dai mutumin ya yi korafin cewar, wasu na amfani da yanayin yunwar da ke damun mutane a gidan gyaran halin na Goron Dutse, wajen rinka bai wa mutane Sinadarin dandano, da Garin Kwaki, kuli-kuli da sauransu.

Kakain Hukumar gyaran halin Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa , sun godewa Allah game da abunda daurarrun suka bayyana da kansu, kuma sun tabbatar da cewa ba a aikata irin laifin da ake zargi.

Musbahu ya yi fatan masu hannu da shuni za su sanya hannunsu wajen taimakawa dararrun da kayan bukatun rayuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
GORON JUMA’A 16/05/2025

GORON JUMA'A 16/05/2025

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version