Zargin Da Ke Tattare Da Kalaman Da ‘Yan Siyasar Philippines Ke Yi Kan Kasar Sin
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Da Ke Tattare Da Kalaman Da ‘Yan Siyasar Philippines Ke Yi Kan Kasar Sin

byCGTN Hausa
1 year ago
Philippines

A baya-bayan nan ne shugaban kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos ya gabatar da wani sako ga kasar Sin a gun taron tattaunawa na Shangri-La karo na 21, inda ya yi barazanar cewa, kasarsa ba za ta yi sassauci kan batun yanki ba. Dangane da haka, wakilin kasar Sin ya bayyana karara cewa, kasar Sin ta dade tana taka tsan-tsan a kan keta haddi da tsokan, amma akwai iyaka, tana fatan wasu kasashe za su fahimci muradunsu, su koma kan teburin tattaunawa da tuntubar juna. 

Tun bayan kulla huldar diflomassiya tsakanin Sin da Philippines a shekarun 1970, gaba daya an kiyaye tasirin batun tekun kudancin kasar Sin kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Amma bayan da gwamnatin Marcos ta hau kan karagar mulki a shekarar 2022, jiragen ruwa na Philippines sun yi ta kutsawa cikin yankin teku na sashen tudun ruwa na Ren’aijiao da tsibirin Huangyan na kasar Sin, lamarin da ya haifar da koma-baya a dangantakar dake tsakanin Sin da Philippines.

  • Firaministan Pakistan: Dangantakar Da Ke Tsakanin Pakistan Da Sin Ba Za Ta Wargaje Ba
  • Sin Tana Son Yin Aiki Tare Da Hukumar IAEA Don Tabbatar Da Shawarar Ci Gaban Duniya Da Shawarar Tsaron Duniya

Hasali ma, halin rashin hankali na gwamnatin Philippines yana da ma’ana. Bobby Tuazon, farfesa a jami’ar Philippines, ya bayyana cewa, Amurka ta dauki Marcos a matsayin wani makami ko ‘yar tsananta na yaki a fakaice. Domin kuwa saboda irin alkawurran tsaro na yaudara da Amurka ta yi, da yawan safarar tsoffin makamai, da kutsawa da tasirin Amurka a Philippines, ya sa gwamnatin Philippines ke son taka rawar gaggafa da kare game da martabar Amurka a harkokin yankin.

A yayin taron tattaunawar ta Shangri-La, an kuma lura cewa, ministan tsaron Amurka, Lloyd Austin, ya bai ce kome ba kan tambayar da Philippines ta yi masa game da matakan da Amurka za ta dauka idan wani abu mai nasaba da yarjejeniyar tsaron hadin gwiwa tsakanin Amurka da Philippines ya wakana, amma ya jaddada cewa, Amurkan za ta karfafa tattaunawa da kasar Sin don tabbatar da cewa irin wannan abu bai faru ba. Akasarin ra’ayin jama’a na ganin cewa, Amurka a fakaice ta bayyana cewa, bai cancanta ta yi fito-na-fito da kasar Sin ba. Ba zai yiwu ba ga Philippines da ta yi duk abin da take so sakamakon goyon bayan Amurka. (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Na Nuna Bajinta Da Gaskiya A Jagorantar Jihar Kaduna – El-Rufai

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version