Umar A Hunkuyi" />

Zargin Kai Wa Buhari Hari A Kebbi: Na Yi Kokarin Gaisawa Da Shi Ne, In ji Muhammad Jamil

A jiya ne lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyara a garin Argungu jihar Kebbi kan kaddamar da bukukuwan gwajin kayan albarkatun gona da ke cikin soma bukukuwan kamun kifi na Argungu .

Inda ake cikin gudanar da bikin wani matashi mai suna Muhammad Jamil da ke garin Guddare da ke cikin karamar hukumar milki ta BirninKebbi yayi kokarin kutse don ya gaisa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda bai samu nasarar yin hakan ba sai jami’an tsaro na farin kaya suka cafke shi .

Bisa ga hakan ne wani bidiyo ke ta yawo kan cewar  matashin yayi yunkarin Kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari  hari a garin na Argungu a jiya da ya kawo ziyara aiki.

Saboda hakan wakilin LEADERSHIP Ayauasabar ya samu jin ta bakin matashin da ake zirgi da Kai wa shugaban kasa hari  ya fara da cewar “ sunana Muhammad Jamil daga kauyen Guddare da ke a cikin karamar hukumar milki ta BirninKebbi cewar ana zirgi na da cewa nayi yunkurin Kai wa  shugaban kasa Muhammadu Buhari  hari a  jiya da ya kawo ziyara a garin Argungu wannan zirgin ba gaskiya ba ne, abin da ya faru shine nayi kokarin gaisawa dashi ne yayi da yake duba kayan albarkatun gona a garin na Argungu”.

Muhammad Jamil ya bayyana hakan ne ga manema labaru a Birnin-Kebbi a jiya kan labarin da ya samu labari  cewa ana zirginsa da cewa yayi yunkarin kai wa  shugaban kasa Muhammadu Buhari hari inda har an harbe ni . Saboda hakan ina son  al’ummar kasar Najeriya ku sani cewar “ Ni Muhammad

Jamil masoyin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kuma da ake cewa jami’an tsaron farin kaya sun bani kashi har da cewa an harbe ni tau ba gaskiya ba ne ina nan lafiya lau batare da wata matsala ba”.

Haka kuma ina son Jama’a su sani cewar” nayi kararu har zuwa jami’a inda na kammala karatun digiri na farko a jami’ar Usmanu Dandodiyo da ke Sakkwato a shekara ta 2016 inda na karanta hakarokin tsarin milki wato (Public Administration) wanda yanzu hakan ina aiki, nayi aure watanni Bakwai da suka gabata”.

Bugu da kari Muhammad Jamil yace “ jami’an tsaron farin kaya sun bincike ni, amma ba tare da wata matsala ba, domin har gidana sun zirarta inda suka tabbatar da cewar “ Ni Muhammad Jamil ba dan ta’adda ba ne  kuma ina da aure da aikin yi” . Haka zakali sun kara gansuwa da cewa ni masoyin Shugaban Buhari ne na gaske na kuma kwashe shekaru ina addu’ar in hadu da Shugaba Buhari Allah bai sa hakan ba sai jiya da ya kawo ziyara a garin Argungu.

“Amma a jiyan ma rashin banbi ka’ida shine ya sanya jami’an tsaron farin kaya kama ni don bincike na, idon ba dan ta’adda ba ne”.  Har ilayau Muhammad Jamil yana kira ga al’ummar kasar Najeriya kan cewa wannan bidiyo da ke yawu dashi karyace da kuma kazafi ne kawai ake yi masa. Ya ci gaba da cewa yanzu hakan daga gida na na fito da ke  Guddare don na gana da manema labaru domin in tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar “ Ni ba dan ta’adda ba ne kuma ban afkawa  shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kamar yadda labaru ke ta yatsuwa a cikin jaridu da kuma kafafen sada zumunci na zamani wato (Social Media) kuma jami’an tsaro sun kama ni a jiyan sun bincike ni har sun salame ni”.

Ya ce “ Tarihin shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikin abin da yasa nake sonsa, domin babu inda tarihinsa ya nuna cewa shi marasa gaskiya ne . Saboda hakan nake sonsa nake bashi goyon baya ga dukkan milkinsa har zuwa yau din nan da nake zantawa da ku.

Exit mobile version