Zauna-gari-banza Sun Kona Gidan Yari A Jihar Imo

Daga Sulaiman Ibrahim

A safiyar yau Litinin, wasu gungun ‘yan ta’adda wadanda ba a ayyana ko suwaye ba, sun afka hedikwatar ‘yan sanda da gidan yari na Jihar Imo.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kone hedikwatar da gidan yarin bayan kubutar da fursunoni sama da 2000 daga gidan yarin, sun kuma hada da kone ababen hawa dake jikin gidan yarin.

Motoci da aka kone a gidan yarin
Daya daga cikin gene-genen da abun ya shafa

Exit mobile version