Zauna-gari-banza Sun Tarwatsa Zaben PDP A Filato

Daga  Sabo Ahmad

’Yan bangar siyasa sun tarwatsar zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP domin tsayar da dan takarar shugaban jam’iyyar na Kanke, a zaben Kananan Hukumomin da za a yi a jihar Filato ranar 18 ga Fabrairun 2018.

’yan bangar sun mamaye Filin wasa na Kwall, inda ake gudanar da wannan zaben, inda suka shiga dukan jami’an zaben na jam’iyyar ta PDP, kuma suka lalata motoci masu yawa.

‘Yan bangar sun cire kunnen Mista Anthony Joro, daya daga cikin jami’an zaben, sannan kuma sun yi wa shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Kanke

Mista Dauda Waptu,dukan kawo wuka, wanda ya yi sanadiyyar ji masa raunuka a fuskarsa.An fara gudanar da zaben lafiya amma lokacin da Waptu ya zo zai kada kuri’arsa sai guri ya hargitse.

Rikicin ya fara ne lokacin da ya ce bai yarda da wasu wakilai su yi zaben ba, saboda ba su yarda da shi ba a matsayin shugaban jam’iyya ba, shi ma wasu suka ce ba za su yarda ya jefa kuri’ar ba saboda ba shi ne shugaban jam’iyyar ba.

Wannan takaddamar ita ta haifar da riciki a gurin zaben, wanda yi sanadiyyar raunata wasu mtane masu yawa da lalata dukiya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Mista Tyopeb Terna, ya tabbatar da faruwar wannan ala’marin, wanda kuma ya ce, a halin yanzu jami’ansu na nan na neman ‘yan bangar siyasar ruwa a jallo.

Saboda haka, sai ya shawarci ‘yan siyasa da su kasance masu bin dokar kasa, ya ce duk wanda aka kama shi da laifin karya doka, za a hukunta shi, domin kuwa babu dalilin da zai sa wasu gungun jama’a su karya doka kuma a kyale su.

Waptu, ya ce, ya yi mamakin yadda aka afkar da wannan rikici, kodayake ya zargi wasu ‘yan majalisa da sa hannu a cikin afkuwar rikicin.

Barkewa rikicin ya girgiza mataimakin shugaban jam’iyyar  PDP na mazabar Sanata ta tsakiyar gundumar filato, Mista Benedict Shignuhul, wanda kuma ya bayyana shi da cewa, babban abin takaici ne, a siyasar jihar Filato. Shi ma ya danganta faruwar rikicin da wasu ‘yan majalisa da ke kokarin tarwatsa jam’iyyar, duk da cewar ita ce ta kais u zuwa matsayin da suke samu a halin yanzu.

Ya ce, maimakon irin wadannan ‘yan majalisa su kawo wa yankin ci gaba, sai dai su haifar da rikice-rikice, saboda wani burin a kashin kansu, wanda ya nua cewa, yin haka ba daidai ba ne.

Shi kuwa, danmajalisa Mista Tim Golu, mai wakiltar Kanke/Pankshin/Kanam a majalisar tarayya ya zargi shugabannin jam’iyyar  wajen haddasa wannan fitina. Domin kuwa ya ce duk da cewar an gaya wa shugabannin jam’iyyar cewa kada a yi zaben a wannan guri, saboda kawai yiwuwar barkewar tashin hankali, suka kafe cewa sai an yi a gurin, to kuma ga abin da ya biyo baya

Saboda haka, sai ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a kama dukkan wadanda suka matsa a yi zaben a wannan guri, kuma a hukunta su, yadda za a kare afkuwar hakan nan gaba.

Exit mobile version