Umar A Hunkuyi" />

Zazzabin Lassa: Katsina Ta Ja Damara, Cewar Gwamnati

A ranar Asabar ce, gwamnatin Jihar Katsina ta shelanta cewa ta farfado da dukkanin wuraren ko-ta-kwana da ke cikin Jihar domin kalubalantar barazanar barkewa da cutar zazzabin Lassa wacce a yanzun haka aka samu rahotannin bullarta a makwabciyar Jihar ta Kano da Kaduna, da kuma wasu Jihohin kasar nan.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Injiniya Nuhu Yakubu Danja, ne ya shaida wa manema labarai hakan a wajen wani taron na manema labaran da ya kira a Katsina, duk da cewa kawo yanzun ba a sami rahoton bullar cutar a Jihar ta Katsina ba, amma dai Jihar ta dauki matakan kare kai domin hanzarta kalubalantar duk wasu matsaloli na lafiya cikin hanzari.

Ya kuma kara da bayanin cewa, Jihar ta farfado da dukkanin wuraren killace wadanda ake tunanin sun yi wata alaka da wadanda cutar ta same su domin kare al’umma.

Ya lissafta wasu daga cikin matakan gaggawan da Jihar ta dauka da suka hada da, tanadar tawaga jami’an lafiya na musamman a kan yaki da cutar, kafa wuraren da za a kebance duk wanda cutar ta bayyana a gare shi, siyo magungunan rigakafi da na maganin cutar ga majinyata.

Sauran matakan da Jihar ta dauka sun hada da, kokarin wayar da kan al’umma ta hanyar malaman Addini, Sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma a kan alamomin cutar da kuma abin da ke sabbaba ta.

Hakanan gwamnatin Jihar tana daukan wani mataki na gwada dukkanin bakin da suke shiga cikin Jihar musamman wadanda suka fito daga makwabciyar Jihar ta Kano.

Kwamishinan ya bayyana cewa duk da kawo yanzun babu wani agaji da Jihar ta samu daga gwamnatin tarayya a kan rigakafin cutar ta Lassa, amma Jihar tana ci gaba da tsara hanyoyin tunkarar cutar ko da za ta yi tunkurin lekwa cikin Jihar.

Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar kula da lafiya ta Jihar ta hannun hukumar kula da lafiya ta Jihar PHCDA, tana yin aiki tare da cibiyar kula da bakin cutuka ta kasa NSCDC, da kuma takwarorin ta daga Jihohin da cutar ta rigaya ta bulla.

Exit mobile version