Ammar Muhammad" />

Zazzabin Lassa Na Ci Gaba Da Hallaka Mutane A Nijeriya

Lassa

Wadansu rahotanni sun bayyana cewa; ya zuwa yanzu fiye da Mutane 300 aka tabbatar da sun kamu da cutar ta Lassa cikin kasa da mako biyu a jihohin Nijeriyar

Hukumar dake kula da cututtuka masu saurin yaduwa a Nijeriya ta NCDC ta sanar da karuwar mutane 37 da suka kamu da cutar Lassa cikin kasa da mako guda a sassan kasarnan.

A jawabinsa babban jami’in hukumar, Chikwe Ihekweazu, ya ce mutanen 37 sun kamu da cutar ta Lassa ne daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Fabarairu.

Mista Ihekweazu ya ce a gwajin da suka gudanar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan nan kan mutane 947 daga jihohi 20 da ake kyautata zaton su na dauke da cutar sun tabbatar da cutar a jikin mutane 324.

Babban jami’in ya nuna cewa, tun bayan sake barkewar cutar a farkon shekarar nan ta 2019 akalla mutane 69 ta hallaka a jihohin Nijeriyar guda 20.

Babban jami’in hukumar, ta NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce daga ranar 8 ga wata mutane 57 ne suka mutu sanadiyyar cutar, amma kawo yanzu adadin ya karu zuwa 69 matakin da ke nuna cewa cutar na ci gaba da yaduwa a sassan Nijeriyar.

Exit mobile version