Hukumomi a jihar Lagos sun tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon cutar zazzabin Lassa wadda bera ke yadawa.
An tabbatar da cutar ne sakamakon binciken da asibitin jami’ar Lagos ta yi a yau Talata.
Babban Darektan asibitin Jami’ar Jihar Lagos (LUTH) Chris Bode, ne ya bayyanawa manema labarai sakamakon binciken da likitocin su ka yi.
Rahotan ya kara da cewa, ma’aikatar lafiya ta jihar na kokarin dakile yaduwar cutar.