Zenith Bank Da Wadansu Biyu Sun Zama Zakara A Kasuwar Hannun Jari

Zenith Bank da Ecobamk da Guaranty Trust Bank sun zama a sahun gaba cikin takwarorinsu goma sha uku a kasuwar hannun jari ta bankuna.

Lokacin da suka samu wannan nasara dai Ecobamk ya fara sayar da hannun jarinsa a kan N13.97, a karshe har sai da ya kai N16.50, GTbank ya samu dagawar hannun jari na kashi 17.8 daga cikin dari,sai  Zenith Bankwanda ya samu kashi 12.1 daga cikin dari.

Karuwar darajar hannun jarin bankunan ya sa an samu karuwa a kasuwar hannun jari ta Najeriya daga bankuna na kashi 12.2 daga cikin dari watau daga 397 zuwa 445.33, wanda ke nuna cewa darajar hannun jarin bankuna  a kasuwar zuba jari ta Najeriya ya karu.

Binciken da Leadership A Yau ta yi yanuna cewa, Zenith Bankya fara da hannun jari a kan N20.89 sannan ya rufe a kan 24.61, sai GTbank da ya fara da N34.82 ya kuma rufe da N39.05, wanda kuma ke da jari mai karfi a kasuwar da ya kai na Naira tiriliyan 1.15. Sai ZenithBankda ke da jarin Naira biliyan 772.8 daga nan sai Ecobank mai jarin Nairabiliyan302.8. Tunidai masu sayen hannun jari keta rububin sayen hannun jarin wadannan bankuna, da tunanin cewa, farashin hannun jarin zai ci gaba da tashi.

Su ma bankunan SkyeBank da UBA daStanbicIBTCna daga cikin jerin bankunan da suka samu karuwar darajar hannunjari a wannan kasuwa. Haka kuma binciken da Leadership A Yau ta gudanar ya nuna cewa, UnityBank da UnionBank da FidelityBank su ne suka zama na baya ga dangi, domin darajar hannun jarinsu ya fadi warwas a wanna kasuwa.

Exit mobile version