Daga Sabo Ahmad Zariya
Binciken da jaridar LEADERSHIP A YAU ta gudanar ya nuna cewa, Hukumomin tara kudaden haraji na jihohi da na gwamnatin tarayya sun karbi harajin naira biliyan 99.26 daga Zenith Bank da wasu masana’antu 15 daga watan Janairu zuwa watan Yuni na bana
Haka kuma binciken jaridar ya nuna an karbi wannan harajin ne daga wasu kamfanoni guda bakwai masu hada-hadar kudi da masa’antu guda biyu da kamfanin sayar da albarkatun man fetur guda hudu, wanda ya kai kimanin naira biliyan
99.26, yayin kamfanoni masu hada-hadar kudi suka bayar da kashi 77.4 daga cikin dari watau naira biliyan 73.5 daga cikin kudin harajin da suka bayar.
Binciken na LEADERSHIP A YAU ya ci gaba da cewa, kamfanoni 16 sun biya harajin naira biliyan 99.9 ga hukumomin tattara haraji daban-daban daga watan Janairu zuwa Yuni na bana. Bankin UBA shi ne kan gaba wajen biyan harajin inda ya biya naira biliyan 15.19, sauran Bankuna sun hada da First Bank naira biliyan 6.1 sai Access Bank Plc, naira biliyan12.6 da Stanbic IBT naira biliyan N5.1 sai Dangote Cement Plc da Dangote Sugar Plc sun bayar da naira milyan 11.5 da naira miliyan N815 daga watan Janairu zuwa Julin bana.
Haka kuma binciken jaridar ya nuna an karbi wannan harajin ne daga wasu kamfanoni guda bakwai masu hada-hadar kudi da masa’antu guda biyu da kamfanin sayar da albarkatun man fetur guda hudu, wanda ya kai kimanin naira biliyan
99.26, yayin kamfanoni masu hada-hadar kudi suka bayar da kashi 77.4 daga cikin dari watau naira biliyan 73.5 daga cikin kudin harajin da suka bayar.
Binciken na LEADERSHIP A YAU ya ci gaba da cewa, kamfanoni 16 sun biya harajin naira biliyan 99.9 ga hukumomin tattara haraji daban-daban daga watan Janairu zuwa Yuni na bana. Bankin UBA shi ne kan gaba wajen biyan harajin inda ya biya naira biliyan 15.19, sauran Bankuna sun hada da First Bank naira biliyan 6.1 sai Access Bank Plc, naira biliyan12.6 da Stanbic IBT naira biliyan N5.1 sai ‘Dangote Cement Plc’ da ‘Dangote Sugar Plc’ sun bayar da naira milyan 11.5 da naira miliyan N815 daga watan Janairu zuwa Julin bana.