Kande Gao Ta CRI Hausa" />

Zhang Weili, Zakarar Gasar Damben UFC Na Fatan Karfafawa ’Yan Mata Gwiwa

A kwanan baya wato ranar 8 ga watan Maris, wata Basiniya ta zama zakarar gasar damben UFC na ajin mafi kankantar nauyi na strawweight, bayan ta doke abokiyar karawarta Joanna Jedrzejczyk ta Poland, yayin gasar dambe ta UFC da aka yi a birnin Las Vegas a gasar UFC ta 248. Sunan macen shi ne Zhang Weili, wadda ta kasance Basiniya ta farko da ta lashe kambin damben UFC na duniya. Yayin da ta zantawa da manema labarai, Zhang ta ce, ta yi kokari sosai wajen zaman zakarar. Kuma tana fatan, za ta iya ba karin ’yan mata kwarin gwiwa domin su zaman jajirtattu masu cimma burinsu.

An haifi Zhang Weili ne a wani karamin kauye na Handan dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin a shekarar 1990. Iyayenta masu aikin hakar kwal ne. A lokacin da take ’yar karama, ta fi yara maza da suke kai daya karfi. Bisa bukatarta, a lokacin da take da shekaru 12, iyayenta suka sa ta a makarantar koyon fasahohin dambe. A matsayinta na daya daga cikin ’yan mata tsiraru dake makarantar, Zhang ta yi kokari wajen jure horo da yin rayuwa cikin yanayi mai tsanani. Ba wani abu ne a wajenta ba, don ta ji rauni yayin da ake horar da su.
Zhang, wadda ta dauka ta kware wajen fada, ta fusata a lokacin da ta gane da dama daga cikin sauran daliban sun fi ta kokari sosai. Sai dai, ko kadan ba ta yi tunanin barin makarantar ba. “Na yi imani idan za ka iya jure wuya mai tsanani, to za ka iya zama mafi kwarewa.” A cewarta. Sakamakon haka, ta kara zage damtse, kuma ta zama daya daga cikin mafi kwarewa a fannin wasan Sanda, wanda ya samo asali daga wasan Kungfu na kasar Sin, ya kunshi naushi da hauri da kokawa. Zhang ta lashe wata gasa a lokacin da take da shekaru 14, inda ta zama zakarar wasan Sanda na matasa, a lardin Hebei.


Daliban makarantar koyon fasahar dambe da suka yi zarra a fasahar Sanda na da zabi da dama bayan sun kammala makarantar: ko su yi aikin dan sanda ko su shiga kungiyar kwararru kan wasan Sanda ko kuma su shiga jami’a. A shekarar 2005, Zhang Weili ta zabi shiga kungiyar kwararru kan wasan Sanda dake Nanjing na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin.
Raunuka su ne abokan gaban ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle. A shekarar 2008 ne Zhang ta yi fama da matsananciyar ciwon kugu kafin ta shiga gasar zakarun wasan Sanda ta kasa. Ba ta samu karbar horon shiga gasar ba, wannan raunin da rashin shiga kasar, ya sa ta kusa rasa aikinta. Zhang Weili ta ce, “Sakamakon raunin da na ji a wancan lokaci, na bar kungiyar kwararru kan wasan Sanda. Iyayena kuma sun fada min cewa, kada in ci gaba da wasan, domin da kyar ake iya samun aiki mai kyau bisa wannan fasahar da nake da ita. A ganinsu, tun da na girma, ya kamata in yi aure.”


Bayan ta zauna a gida na wani lokaci, Zhang ta je Beijing domin neman aikin yi. Ta yi aiki a wata makarantar yara a matsayin malama, sai kuma ta yi aikin kashiya a wani otel. Ta ji kamar burinta na fafatawa a dambe na kokarin zama tarihi. “A hakika dai, ba na son yin watsi da wannan burina ba. A wasu lokuta, yayin da na samu labarai kan yadda abokan dambena ke shiga gasanni, raina kan baci”, a cewarta.
A shekarar 2010, Zhang ta je wani wurin motsa jiki, domin neman aiki yi. Ta yi mamakin ganin sashen dambe. Sai ta tambayi manajan idan za ta iya bita a lokacin da babu wanda ke amfani da wurin. Manajan ya amince da ita, ita kuma sai ta amince ta karbi aikin, ta kuma fara zuwa a washegari. Saboda tsabar farin ciki, ta ma manta ta tambayi nawa za a bata a matsayin albashi. Zhang ta furta cewa, “A wancan lokaci, na kan yi horo da kaina a safe, kuma na fara aikin bita da yamma. Kullum na kan tashi kimanin karfe 6 na sassafe, da kuma bar aiki kimanin karfe 10 da dare. Bayan da na koma gida, sai in yi barci da karfe 12. Na yi hakan a ko wace rana, har bayan shekaru biyu. Amma ko da hakan, ban yi tsammanin cewa, wai rayuwata za ta tsaya a kan wannan matakin ba, bai kamata in ci gaba da hakan ba.”
A lokacin, ’yan wasan Sinawa da suka hada da maza da mata, ciki har da Zhang Tiequan da Wu Haotian, sun shiga gasar zakarun UFC. Hukumar shirya gasar UFC wadda aka kafa a shekarar 1993, ita ce mai shirya gasar dambe ta mata da maza.


A wata rana, Zhang Wei Li ta kasance abokiyar damben Wu Haotian. Cai Xuejun, daya ne daga cikin manajoji na farko na ’yan wasan dambe, kuma yana kallon yadda Zhang ke taimakon Wu wurin bita. Cai ya tuna da cewa, “A karon farko da na ga Zhang, mace mai tsawon mita 1.6, na gano cewa, ba ta jin tsoron dambe, tana iya nuna karfi kamar maza. Kokarinta ya burge ni.” Cai Xuejun yana jin Zhang Weili za ta iya zama kwararriya, idan ta yi amfani da gogewarsa na horar da ’yan wasa.
“A lokacin, aka fara wasu kananan shirye-shiryen mata ’yan wasan dambe a kasar Sin. Kuma na ga yadda Ronda Rousey, zakarar UFC ke nuna kwarewar mata a wannan fannin. Lallai lamarin da ya karfafa zuciyata sosai. Tabbas zan iya”, in ji Zhang. Matukar kokarin da ta yi ya sa Cai Xuejun ya sanya Zhang Weili a wata gasar dambe ta mata a shekarar 2013. Sai dai ba ta yi nasara ba, saboda ba ta goge ba. Zhang ba ta fidda rai ba. Sai ta wallafa a shafinta na sada zumunta na Intanet na Weibo cewa, “na yi imanin idan ban fidda rai ba, idan kuma na dau darasi daga rashin nasarar, zan iya shiga gasar UFC.”
Cai Xuejun ya fada mata cewa, dole ne ta bar aiki ta mayar da hankali wajen samun horo idan har tana son lashe gasa. A don haka, Zhang ta bar aikinta na wurin motsa jiki ta zama kwararriyar ’yar wasan dambe.
Sai dai an yi rashin nasara, Zhang Weili ta ji rauni a kugunta yayin horo. Tsawon watanni 9, Zhang ba ta iya gudu kuma ba ta iya tsalle. Cai ya kai ta wajen da yake bayar da horo domin koyar da ita dabarun farfadowa, da kuma yadda za ta shirya da cin abinci mai gina jiki. Da taimakon Cai, Zhang ta farfado ta kuma koma daukar horo. Zhang ta waiwayi cewa, “Wata rana yayin horo, na yi kuskuren buge kashin dake saman idon mai horona wanda ya sa wajen fara jini. Ina so na daina karbar horon, amma sai ya dage sai na ci gaba. Ina kuka ina samun horo har zuwa karshe bayan mintoci biyar. Mutanen dake kewaye da ni na namijin kokari. Ba ni da dalilin gajiyawa.”
A shekarar 2015 ta shiga kungiyar ’yan dambe ta Kulun, wadda aka kafa a 2014, da a yanzu kuma ta zama daya daga cikin manyan kungiyoyin dambe na duniya. Zhang ta samu nasarori 16 da lakabin Kunlun 2 na ajin marasa nauyi na Strawweight da flyweight a lokacin da ta cika shekaru 27 da haihuwa. Kokarinta da irin wahalar da ta jure, su ne suka kai ta ga samun nasara. Zhang ta ce, “An taba tambayata cewa, wane irin mutumiya ce kike so ki kasance? Na amsa da cewa, muddin aka ambaci wasan dambe, to za a tuna da ni, ina so in kasance irin wannan. Sa’an nan kuma samun damar shiga cikin ’yan wasan UFC ya bude min wani sabon shafi.”
A watan Mayun 2018, Zhang ta zama daya daga cikin ’yan wasan UFC. Zhang ta yi ammana cewa, abu mafi kyau shi ne cin nasara kan abokin fada tun da wuri, domin rage hadari da tsananin raunukansa.
Bayan ta zama ’yar wasan UFC, Zhang ta yi nasara a gasanni 3, kuma a watan Maris na 2019, ta zama daya daga cikin ’yan dambe 10 dake kan gaba a ajin Strawweight na UFC.
Duk da haka, wasu ’yan wasan UFC ba sa son karawa da Zhang, saboda a ganinsu, ba ta shahara ba. A ganinsu, yin nasara a kanta ba zai amfana musu ba, amma shan kaye a hannunta, zai kunyata su.
Wata rana, a watan Yunin 2019, Cai Xuejun ya shaida mata cewa, “za ki kara da Jessica Andrade, zakarar UFC”. A wannan dare, farin ciki ya hana Zhang barci. Kawai so take ta tashi ta yi bita. Ta dade tana mafarkin karawa da Jessica Andrade, zakarar kasar Brazil. Ga shi yanzu za su fafata.
Yayin gasar, an sanya ’yan wasan ne a waje mai kusurwa 8, wanda ya yi kama da keji. Don haka ake kiran gasar a matsayin gasar keji. An gudanar da wasan ne a cibiyar wasanni ta Universiade dake birnin Shenzhen na kasar Sin. Zhang ta shiga gasar ne a matsayin wadda ake ganin ba za ta yi nasara ba, amma bayan doke-doke da gwiwa da naushi, Zhang ta doke Andrade. Fadan ya shafe dakiku 42 kadai. Zhang ta zama zakarar UFC na ajin Strawweight. Wannan kuma ita ce nasara ta 20 da ta samu a jere. Ta zamo zakarar UFC ta farko daga kasar Sin da ma Asiya a duniya. Zhang ta bayyana a hirar da aka yi da ita bayan wasan, cewar “Suna na Zhang Weili, ni Basiniya ce, ku tuna da ni!”
Nan take bayan ta yi nasara, miliyoyin sakonni daga kasashe daban daban na duk duniya, sun sa Zhang ta zama abun labari a intanet, kuma da yawa daga cikin Sinawa suka yi sha’awar shiga wasannin dambe da gasar UFC. A matsayin ’yar dambe, Zhang ta taimaka wajen fadada shaharar wasan a kasar Sin a 2019, inda aka mata lakabi da Mace ’yar wasan dambe ta shekarar 2019 ta Yahoo.
Haka kuma, a cikin gasar damben UFC na ajin mafi kankantar nauyi da aka yi a kwanan baya, wato a ranar 8 ga watan Maris na shekarar bana, Zhang Weili ta sake zama zakarar gasar, bayan ta doke abokiyar karawar ta Joanna Jedrzejczyk daga kasar Poland. Wannan kuma ita ce nasara ta 21 da ta samu a jere.
Zhang ta zama abun koyi ga ’yan damben kasar Sin, kuma ta zama abun koyi ga ’yan mata. A ganinta, mata daidai suke da maza. Mata za su iya cimma abun da maza suka cimma. Mata za su iya abubuwa da dama. Bai kamata a rika bayyana mace a matsayin mai rauni ba. Dole ne ta zama jaruma, jajirtacciya, hazika, ta kuma tsaya da kafarta. Zhang tana mai cewa, “Wannan abu ne da nake matukar sha’awa a kai, kuma bisa kokarina, na cimma buri, da kuma shaida cewa, mu mata muna iya samun nazara a fannin wasan dambe. Idan labarina zai sa mutane su daina saduda duk wahalar da ke gabansu, to shi ne abu mafi daraja da ma’ana gare ni da kasancewata a wannan duniya.”

Exit mobile version