Zhao Ai: Raya Hanyar Siliki Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba, Wata Hanya Ce Mai Dacewa Wajen Bayyana Labarun Kasar Sin Da Kyau

Daga CRI Hausa,

An bude taron kasa da kasa game da “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina aka fito, ina kuma aka dosa—— Sauye-sauyen duniya a shekaru 100 da kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar” a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, taron da ke gudana daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan.

Zhao Ai, mataimakin shugaba kuma babban darektan cibiyar nazarin yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin, kuma tsohon jami’in kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya zanta da wakilin CMG, inda ya nuna cewa, wajibi ne a raya hanyar siliki ba tare da gurbata muhalli ba cikin hadin gwiwar sassa daban daban, a fannonin daidaita sauyin yanayi, rage radadin bala’u daga indallahi, kiyaye muhalli da rage talauci. (Tasallah Yuan)

 

Exit mobile version