Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home WASANNI

Zidane Ne Wanda Ya Dace Da Real Madrid

by Sulaiman Ibrahim
March 27, 2021
in WASANNI
2 min read
Zidane Ne Wanda Ya Dace Da Real Madrid
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abba Ibrahim Wada

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da tafiya da mai koyar da ‘yan wasanta, Zinadine Zidane, har sai lokacin da abubuwa suka koma dai-dai saboda har yanzu shine ya dace da kungiyar.
Perez ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a bayan wani taron gaggawa da kungiyar ta Real Madrid ta shirya akan masu zuba jari a kokarin da kungiyar take yin a samo sababbin hanyoyin kudin shiga.
A kwanakin baya shima daraktan  gudanarwar kungiyar , Betroguenos, ya bayyana cewa kungiyar ba zata kori kociyan kungiyar Zinadine Zidane ba duk da cewa ana samun rashin nasara a halin da ake ciki yana mai cewa zasu ci gaba da bashi goyon baya.
Betroguenos  ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a daidai lokacin da kociyan kungiyar yake kwance yana jiyyar cutar Korona data kamashi bayan an gwada shi kwana daya bayan an fitar da kungiyar daga gasar Copa Del Rey.
Shima tsohon dan wasan gaba na kungiyar, Raul Gonzales, ya bayyana cewa mai koyarwa Zinadine Zidane shine wanda ya cancanta ta ci gaba da zama a kungiyar Real Madrid saboda babu kamarsa yanzu.
Yanzu haka dai Zidane na fuskantar matsin lambar lashe gasar La Liga, wadda kungiyar ke matsayi na uku da maki 60, maki 6 tsakaninta Atletico Madrid, yayin da kuma Barcelona babbar abokiyar hamayyar Real Madrid din ke biye da ita a matsayi na biyu da maki 62
Rabon da Real Madrid ta kare kakar wasa ba tare da lashe kofi ba tun kakar wasa ta 2009 zuwa 2010, ita kuwa Barcelona ba ta ci kofi ko daya ba sai dai a yanzu kofunan da ke gaban Real Madrid sun hada da na Champions League, wanda ta kai karawar zagaye na kusa dana kusa dana karshe za kuma ta fafata da Liberpool.
Koda yake masu hasashe ba sa saka Real Madrid cikin wadanda ake sa ran za ta iya lashe kofin na zakarun Turai na bana kuma hakan ya biyo bayan kasa kokari da kungiyar ta yi a karawar cikin rukuni da sauran wasannin da take yi a bana.
Sannan kuma wannan ne karon farko da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, wadda itace ta lashe La liga a shekarar data gabata ta yi rashin nasara a hannun Alcoyano, wadda ta fitar da ita a gasar Copa Del Rry tun bayan shekara ta 1951 a wasa uku da suka yi a gasar

SendShareTweetShare
Previous Post

Za A Samu Dan Kwallon Da Zaifi Ronaldo A Nan Gaba

Next Post

Willian Zai Taimaka Mana Wajen Cikar Burinmu – Arteta

RelatedPosts

Rohr

Muna Da Manyan ‘Yan Wasan Da Za Su Lashe Mana Kofin Afrika -Rohr

by Muhammad
16 hours ago
0

Kociyan tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Gernot Rohr, ya bayyana...

Ahmad Musa

Me Ya Sa Ahmad Musa Ya Koma Kano Pillars?

by Muhammad
16 hours ago
0

Tuni aka kaddamar da kyaftindin tawagar kwallon kafar Super Eagels...

Turai

A Birnin Roma Za A Buga Wasan Karshe Na Kofin Nahiyar Turai

by Muhammad
16 hours ago
0

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta...

Next Post
Willian Zai Taimaka Mana Wajen Cikar Burinmu – Arteta

Willian Zai Taimaka Mana Wajen Cikar Burinmu - Arteta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version