Abba Ibrahim Wada" />

Zidane Ya Ba Wa Madrid Damar Sayo Kante

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bukaci Real Madrid din data kawo masa dan wasa N’Golo Kante, wanda Chelsea take shirin sayar dashi a kakar wasa mai zuwa

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai ta shirya sayar da N’Golo Kante idan har kungiyoyin Paris Saint German da Real Madrid za su iya biyan abinda kungiyar zata bukata kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Zidane ya na fatan Real Madrid ta sayi Kante domin ya dinga taimakawa Casemiro ko kuma ya zama kishiyarsa kamar yadda wasu lokutan yake samun matsala ta jin ciwo ko kuma dakatarwa sai dai kuma Kante ba zai iya zaman benci ba.

Kante, dan kasar Faransa, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ne a shekara ta 2016 kuma tun bayan komawarsa ya bayyana kansa a duniya a matsayin babban dan wasan tsakiya kuma ya lashe kofin firimiya daya da kofin kalubale da kuma Europa.

Sai dai duk da irin kwarewar dan wasan kociyan kungiyar kwallon kafar ta Chelsea, Frank Lampard ya fara tunanin rabuwa da dan wasan mai shekara 29 a duniya saboda yana fatan sayan matasan ‘yan wasa masu jini a jiki.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, yana fatan ganin ya dauki dan wasan wanda ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Leceister City domin ya hada shi da Paul Pogba da Kylian Mbappe, wadanda  Real Madrid din take tunanin dauka.

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta PSG tana bibiyar dan wasan kuma tana ganin idan har Chelsea ta saka dan wasan a kasuwa zata iya biyan abinda ake bukata domin mayar da dan wasan kasar Faransa ya ci gaba da buga wasa.

Kawo yanzu dai Kante yana da ragowar kwantiragin shekara uku a kungiyar Chelsea kuma kociyan kungiyar yana son shugabannin Chelsea su bashi kudi domin ya sayi matasan ‘yan wasan da zasu karawa kungiyar karfi a kakar wasa mai zuwa

Exit mobile version