Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa dole kungiyarsa tana bukatar dan wasa mai zura kwallo a raga biyo bayan canjaras din da tawagar tasa ta buga a daren Asabar da kungiyar Osasuna a gasar La liga.
Real Madrid tana ci gaba da saka kaimi domin ganin ta samu nasarar lashe gasar La liga ta kasar Ingila kuma da ace ta samu nasara a wasan na ranar Asabar zata zama ta daya akan teburin gasar sai dai duk da haka kungiyar za ta buga gasa uku cikin watan Janairun shekara ta 2021 da suka hada da La Liga da Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey.
Real Madrid wadda take ta biyu a teburin La liga ta shiga shekarar 2021 da kafar dama, bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Celta Bigo daci 2-0 a gasar Spaniya ranar biyu ga watan Janairu a filin wasa na Alfredo Di Stefano sai dai ta kasa doe Osasuna a wannan satin da ya gabata.
A watan na Janairu kungiyar za ta fafata a karawa uku a La Liga, da daya a gasar Spanish Super Cup wanda ta lashe a bara a Saudiyya da kuma fafatawa a gasar cin kofin Copa del Rey wato gasar cin kofin kalubale na kasar.
“Tabbas akwai karancin zura kwallo a raga a wannan tawagar tamu saboda haka muma fatan nan gaba kadan zamu samu dan wasan gaba wanda zai taimaka mana saboda zura kwallo a raga yayi kadan a wannan kungiyar” in ji Zidane
Sai dai an tambayi mai koyarwar ko zasu shiga kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a wannan watan na Janairu domin sayan dan wasan gaba amma Zidane din bai fayyace abinda yake nufi ba hakan yasa ake ganin watakila kungiyar ta iya sayan dan wasan gaba guda daya ko kuma ta karbi aro zuwa karshen kaka.
A kwanakin baya kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa ‘yan wasan kungiyar za suyi iya kokarinsu wajen ganin sun farantawa magoya bayan kungiyar rai ta hanyar lashe kofi duk da cewa har kawo yanzu ‘yan wasa basa shiga kallon wasan.
Zidane ya kalubalanci ‘yan wasan da su dage wajen zura kwallo a raga domin hakkin kowanne dan wasa ne yayi kokarin zura kwallo a raga domin taimakawa kungiyara wajen cikar burinta na lashe kofi a bana.