Abba Ibrahim Wada" />

Zidane Ya Hakura Da Sayen Pogba

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya janye kudirinsa na ganin  kungiyar ta yi cinikin dan wasa Paul Pogba daga Manchester United bayan gaza cimma matsaya tsawon lokaci.

Pogba dan Faransa, wanda tun a waccan kaka, ake tattaunawa game da yiwuwar komawarsa Real Madrid amma kuma aka gaza cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu, inda tsohon dan wasan na Juventus ya ci gaba da zama a Manchester United tare da fuskanta tarin raunuka a wannan kaka.

Wasu bayanai sun nuna cewa yanzu haka Zidane a janye daga bukatar ta sayen Pogba yayinda zai maye gurbinsa da wani dan wasa daban yayin kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu da za’a bude.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa wargajewar cinikin ya biyo bayan farashin yuro miliyan 180 da Manchester United ta sanya akan Pogba wanda shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce bai shirya biyan dan wasan farashin ba.

Sai dai a tsakiyar wannan satin aka hango Zidane da Pogba a kasar Hadaddiyar daular Larabawa suna Magana a wani wajen shakatawa sai dai kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa wannan hoton da aka gani baya nuna cewa akwai wata matsala.

Banda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, itama tsohuwar kungiyar wato Juventus, ta nuna sha’awarta ta ganin ta sake sayan dan wasan wanda ya lashe gasar cin kofin duniyar da aka buga a shekarar data gabata a kasar Rasha

Exit mobile version