Kociyan ’yan wasan Real Madrid, dan kasar Faransa, Zinedine Zidane ya ce, ya na son kungiyar tasa ta kawo masa Aledis Sanches na kungiyar Arsenal a kakar wasa mai zuwa.
A karshen wannan kakar ne dai kwantaragin dan wasan zai kare da Arsenal bayan da ya ki sake sabunta yarjejeniya da kungiyar bayan da kungiyar ta ki amincewa da albashin da ya ke bukata.
A karshen watan Agusta ne dai Manchester City ta kusa daukar dan was an, sai dai cinikin ya gamu da cikas bayan da Arsenal din ta rasa wanda zai maye gurbinsa.
Rahoton ya ce, Zidane ya sanar da shugaban gudanarwar kungiyar cewa ya na son dan wasan a karshen wannan kakar wanda a ke tunanin zai maye gurbin Karim Benzema wanda shi ma a ke danganta shi da komawa Arsenal din.
Kungiyoyin PSG da Manchester United da City da Bayern Munich su ma su na zawarcin dan wasan dan shekara 29 a duniya haifaffen kasar Chile.