Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya sake caccakar ‘yan jaridun kasar Sipaniya a karo na biyu sannan ya bukaci da su rika fadin gaskiya idan zasu rubuta labari akan Real Madrid sannan ya ce har yanzu Real Madrid tana fafatawa a gasar La Liga kuma zasu ci gaba da cin wasanni domin samun nasarar lashe gasar ta bana.
Real Madrid tana mataki na uku akan teburin gasar La liga, inda take bayan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, wadda ke saman teburin da maki shida kuma duk da haka Real Madrid ta fi ta yawan buga wasa sannan yadda kungiyar ta gaza yin katabus a ‘yan kwanakin nan ya sa kafafen watsa labari sun soma caccakar Zidane, dan kasar Faransa da nuna gazawa.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana fama da koma baya a wannan kakar wanda hakan yasa aka fitar da ita daga gasar cin kofin Copa Del Rey duk da cewa wasu suna ganin rashin ‘yan wasa masu lafiya ne yake kawowa kungiyar tarnaki.
“Abin da yake ba ni dariya shi ne yadda kuke tambaya ta me ya sa nake fushi bai kamata ‘yan jarida ku rika yi min abin da kuke yi min ba mun dauki kofi a kakar wasan da ta wuce domin haka ina ganin ya kamata ku mutunta ni” in ji Zidane a taron manema labarai a kwanakin baya.
Ya kara da cewa “Ba wai mun shekara 10 ba ne (da daukar kofi), a kakar wasan da ta wuce ne kuma akalla ya kamata ku mutunta mu kan abubuwan da muka samu nasara a kansu ku (‘yan jarida) kun cika surutu sannan me ya sa ba za ku kalle ni ido da ido ku gaya min cewa kuna so a kore ni daga kungiyar nan ba, ba a bayan idona ba.”
An sake nada Zidane a matsayin kociyan Real Madrid a watan Maris na shekarar 2019, bayan ya jagoranci kungiyar wajen daukar kofin Zakarun Turai sau uku a jere da kuma kofin lig a kakar wasa ta shekarar 2016 zuwa 2017 lokacin shugabancinsa na farko.
Dan kasar Faransa mai shekara 48 a duniya zai jagoranci kungiyar a fafatawa da kungiyar da ke kasan teburin gasar La Liga Huesca bayan Real Madrid ta sha kashi a hannu Lebante koda yake bai halarci wasan ba saboda ya kamu da cutar korona
“An killace ni tsawon mako biyu, na matsu na fito na kuma nuna wa duniya cewa zan jajirce har zuwa karshe kuma yanzu na dawo domin ci gaba da jagorantar wannan kungiya zuwa ga nasara kamar yadda na saba a baya,” in ji shi.
Sergio Ramos bai fafata ba a wasan da kungiyar ta buga saboda raunin da ya ji, a yayin da Zidane ya sanya masu tsaron raga uku a tawagarsa mai mutum 17 kuma ‘yan wasa Eden Hazard da Dani Carbajal da Federico Balberde da Rodrygo da Lucas Vazquez su ma ba su shiga karawar ba saboda jinya, ya yin da aka dakatar da Eder Militao.